Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wani wurin da zasu dinga taruwa a wurin, babu siye da siyarwa a cikinsa suna ɗaukar abinda suke so daga gare shi, suna zuwa wurin gwargwdan kwana bakwai, sai iskar arewa ta taso, sai ta motsa a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa, sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ƙawa, sai iyalansu su ce musu: Wallahi haƙiƙa a bayanmu kun ƙara kyau da ƙawa, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu.
- Bayanin cewa 'yan aljanna suna samun ƙaruwar kyau da ƙawa.
- Hadisan suna sawa mutum kwaɗayi a cikin aiki nagari wanda ake taka shi zuwa wannan gidan.
- An keɓanci iskar arewa da ambato ne; domin cewa ita ta kasance mafi kyan iska a wurin larabawa yayin da take zuwa da alheri da kuma ruwa.
- Kwaɗaitarwa akan kira zuwa ga Allah ta hanyar kwaɗaitar da aljanna da kuma ni'imarta.
صحيح مسلم (4/ 2178) (2833). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1290). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 347). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مُبَارَك (ص1088). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 731).