Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «حُجِبَتِ النَّارُ بِالشَّهَوَاتِ، وَحُجِبَتِ الْجَنَّةُ بِالْمَكَارِهِ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wuta abar kewayewace da al'amuran da rai take son sha'awrsu na aikata abubuwan da aka haramta, ko takaitawa a wajibai; Duk wanda ya bi son ransa a hakan to ya cancanci wuta, Kuma cewa Aljanna abar kewayewace da al'amuran da rai take kin su; kamar lazimta akan abubuwan da aka umarta da barin abubuwan da aka haramta, da hakuri akan hakan, idan ya kutsa kuma ya yaki ransa a hakan to ya cancanci shiga Aljanna.

Fa’idoji
  1. Daga sabubban afkawa a sha'awowi kawatawar Shaidan abin ki da mummuna, har rai ya gan shi mai kyau ne, sai ya karkata zuwa gare shi.
  2. Umarni da nisantar sha'awowin da aka haramta; domin cewa su hanya ce zuwa wuta, da kuma hakuri akan abubuwan ki; domin cewa su hanya ce ta zuwa Aljanna.
  3. Falalar yakar rai ko kokari a ibada, da kuma hakuri akan abubuwan ki da wahalar da ke kewaye ayyukan biyayya.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 102) (6487). صحيح مسلم (4/ 2174) (2822). سنن أبي داود (7/ 122) (4744). سنن الترمذي (4/ 274) (2560). سنن النسائي (7/ 3) (3763). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 449). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 87). المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي (17/ 165). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 183). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (1/ 134).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com