Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِذْ سَمِعَ وَجْبَةً، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَدْرُونَ مَا هَذَا؟» قَالَ: قُلْنَا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «هَذَا حَجَرٌ رُمِيَ بِهِ فِي النَّارِ مُنْذُ سَبْعِينَ خَرِيفًا، فَهُوَ يَهْوِي فِي النَّارِ الْآنَ حَتَّى انْتَهَى إِلَى قَعْرِهَا».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayin da ya ji wata kara, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san mene ne wannan?" ya ce: Muka ce: Allah da ManzonSa ne mafi sani, ya ce: "Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji wani sauti (kara) mai tsoratarwa kamar faɗuwar wani jiki daga jikkuna, sai ya tambayi waɗanda ke tare da shi cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da wannan karar, sai suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai wanann karar da kuka ji ta ta wani dutse ce da aka yi jifa da shi daga gefen Jahannama tun shekara saba'in, shi yana sauka yana faɗawa a cikinta, har sai ya kai karshenta a yanzu lokacin da kuka ji sautin.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan tanadi ga ranar lahira da aiki na gari, da gargaɗarwa daga Jahannama.
  2. An so danganta ilimi zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - cikin abinda babu wani sani ga mutum akan shi.
  3. Zaburar da malami himmatuwa da faɗaka kafin yin bayani; dan ya zama mafi jawo hankali wurin fahimtarwa.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2184) (2844). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 476). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 369). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 414).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com