An cewa Usama ɗan Zaid Allah - Ya yarda da su - Shin baka shiga wurin Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ba ka yi masa magana cikin abinda yake faruwa na fitina tsakanin mutane da kokari a kasheta gabaɗayanta, sai ya sananar da su cewa shi ya yi masa magana a sirri dan neman maslaha badan tada fitina ba, manufarsa cewa shi ba ya son bayyanar da inkari ga sarakuna a cikin jama'a, sai ya zama sababi na rena khalifa, kuma shi ne kofar fitina da sharri ba zan zama farkon wanda zai buɗeta ba. Sannan Usama - Allah Ya yarda da su - ya ce: Shi yana yi wa sarakuna nasiha a boye kuma ba ya yi wa wani mujamala koda sarki ne, kuma ba ya yi musu fadanci sai ya yabe su a gabansu da karya, hakan bayan ya ji daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi za’a zo da wani mutum ranar alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin (kayan) cikinsa su fito daga cikinsa da gaggawa saboda tsananin zafi da tsananin azaba, sai ya kewaya da 'ya'yan cikinsa yana wannan halin kamar kewayawar jaki a gefan dutsen nikansa, sai 'yan wuta su taru a gefansa kamar sarkar data kewaye shi, sai su tambaye shi : Ya wane, shin ba kaine ka kasance kana umartarmu da aikin alheri ba kuma kake hanamu abin ki ba?! Sai ya ce: Lallai ni na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki kuma ina aikata shi.
- Asali a cikin nasiha ga shugabanni ta kasance tsakaninsa da su ne, kuma kada mutum ya yaɗa abin a gaban gamagarin mutane.
- Narko mai tsanani na azaba ga wanda maganarsa ta sabawa aikinsa.
- Ladabi tare da sarakuna (shugabani) da tausasa musu, da umartarsu da aikin alheri, da kuma hanasu abin ki.
- Zargin yi wa shugabanni mujamala a kan gaskiya, da kuma bayyanar da abinda ya boye sabaninsa kamar mai fadanci da karya.
صحيح البخاري (4/ 121) (3267). صحيح مسلم (4/ 2290) (2989). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (4/ 143). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 358). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص156). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 220).