Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Musulunci ya fara yana baƙo, kuma zai dawo baƙo, aljanna ta tabbata ga baƙi».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Musulunci ya fara yana baƙo a cikin ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙarancin ma'abotansa, kuma zai dawo yana baƙo saboda ƙarancin wanda zai tsayu da shi, to farin ciki, kuma madalla ga baƙi, da farin ciki da sanyin ido gare su.
Fa’idoji
Bada bayanin kasantuwar baƙuntar Musulunci bayan yaɗuwarsa da kuma shahararsa.
A cikinsa akwai alama daga alamomin Annabci, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari da abinda zai faru a bayansa, sai ya faru kamar yadda ya bada labari da shi.
Falalar wanda ya ƙauracewa ƙasarsa da danginsa; saboda Musulunci, kuma lallai aljanna ta tabbata agare shi.
Baƙi su ne waɗanda suke gyaruwa idan mutane suka ɓaci, kuma sune waɗanda suke gyara abinda mutane suka ɓata.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 130) (145).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (4/ 142).
إكمال المعلم بفوائد مسلم (1/ 456).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com