Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne
Daga Ubaidullahi ɗan Mihsan al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa yaku musulmai duk wanda ya wayi gari a cikinku yana mai lafiyayye kuɓutacce a cikin jikinsa daga illoli da cututtuka, kuma yana amintacce a cikin ransa da iyalansa da hanyarsa ba ya tsoro, kuma yana da isasshen abin cin yininsa na halal; to kamar an tattara masa duniya ne gabaɗayanta.
Fa’idoji
Bayanin larurar buƙatuwar mutum ga lafiya da aminci da kuma abinci.
Ya wajaba akan bawa ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma ya gode maSa akan waɗannan ni'imomin.
Kwaɗaitarwa akan wadatar zuci da kuma gujewa duniya.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 167) (2346).
سنن ابن ماجه (5/ 253) (4141).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 570).
التنوير شرح الجامع الصغير، لمحمد الصنعاني (10/ 110).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com