عن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما: عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه كان إذا دخل المسجد قال: «أعوذ بالله العظيم، وبوجهه الكريم، وسلطانه القديم، من الشيطان الرَّجِيم»، قال: أَقَطُّ؟ قلت: نعم، قال: فإذا قال ذلك قال الشيطان: حُفِظَ منِّي سائر اليوم.
Daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Ass - Allah Ya yarda da su -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskarSa Mai girma, da sarautarSa daɗaɗɗiya, daga Shaiɗan abin jefewa", Ya ce: Wannan kawai? na ce: Eh, ya ce: Idan ya ce haka Shaiɗan zai ce : an kiyaye shi daga gareni ragowar yinin.
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga masallaci zai ce: (Ina neman tsarin Allah Mai girma) Ina neman tsari ina fakewa ga Allah da kuma siffofinSa (Da fuskarSa mai kyauta) Mai kyauta Mai bayarwa, (Da sarautarSa) RinjayenSa da ikonSa da rinjayenSa akan wanda ya yi nufi daga halittarSa (Madawwami) na tun fi azal na har abada (Daga Shaiɗan abin jefewa) Abin nisantarwa abin korewa daga rahamar Allah, Wato; Ya Allah Ka kiyayeni daga wasiwasinsa da halakarwarsa da tsarinsa da haɗarinsa da ƙawacensa da ɓatarwarsa, domin shi ne sababi a ɓatarwa mai sa halakarwa da jahilci, Aka cewa Abdullahi ɗan Amr "Shin shike nan?" Wato: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wannan kadai? Ya ce: Eh.
Idan mai shiga masallaci ya faɗi wannan addu'ar; Shaiɗan zai ce : Haƙiƙa an kiyaye ran wannan mai shigowar daga gareni dukkanin lokaci, yininsa da darensa.
Fa’idoji
Falalar yin addu'a da wannan zikirin a lokacin shiga masallaci, kuma cewa shi ana kiyaye mai faɗarta daga Shaiɗan a ragowar yininsa.
Gargaɗarwa daga Shaiɗan, kuma cewa shi yana jiran musulmi; dan ɓatar da shi da kuma halaka shi.
Mutum yana samun kiyayewa daga halakarwar Shaiɗan da karkatarwarsa gwargwadon abinda yake tsayuwa a zuciyarsa na imani da Allah da halarto wannan addu'ar da gasgatawarsa ga alƙawarin Allah abin wanda ta tabbata akansa.
Madogara
سنن أبي داود (1/ 349) (466).
شرح سنن أبي داود، لبدر الدين العيني (2/ 374).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (2/ 627).
Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da al'ummarsa addu'ar da ake faɗa a yayin shiga masallaci: (Ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarKa), sai ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaka masa hanyoyin rahamarSa, idan ya yi nufin fita, to, ya ce: (Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa), sai ya roƙi Allah daga falalarSa da ƙarin kyautatawarSa daga arziki na halal.
Fa’idoji
An so wannan adddu'ar a yayin shiga masallaci da fita daga cikinsa.
Keɓance ambaton rahama a shiga, da falala a fita: saboda mai shiga ya shagalta da abin da zai kusanto da shi zuwa ga Allah da kuma aljannarSa, sai ya dace da ya ambaci rahama, idan ya fita zai tafi a ban ƙasa don neman falalar Allah da arziki, sai ya dace da ambaton falala.
Waɗannan zikiran ana faɗinsu ne yayin nufin shiga masallaci, da yayin nufin fita daga cikinsa.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 494) (713)، الكاشف عن حقائق السُّنن (3/935)، فيض القدير (1/ 336)، ذخيرة العقبى (9/153).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com