Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا لَقِيَ أَحَدُكُمْ أَخَاهُ فَلْيُسَلِّمْ عَلَيْهِ، فَإِنْ حَالَتْ بَيْنَهُمَا شَجَرَةٌ أَوْ جِدَارٌ أَوْ حَجَرٌ ثُمَّ لَقِيَهُ فَلْيُسَلِّمْ عَلَيْهِ أَيْضًا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da musulmi da yin sallama ga ɗan uwansa musulmi duk lokacin da ya haɗu da shi, koda sun kasance suna tafiya tare ne kuma wani abu mai rabawa ya raba su, kamar bishiya ko gini ko babban dutse, sannan ya haɗu da shi bayan nan to ya yi masa sallama karo na biyu.

Fa’idoji
  1. An so yaɗa sallama, kuma a maimaitata a lokacin canjin hali.
  2. Tsananin kwaɗayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan yaɗa sunnar sallama da kai matuƙa a cikinta; dan abinda ke cikinta na jawo soyayya da hada tsakanin musulmai.
  3. Sallama ita ce faɗin: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata a gareku) ko: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh, wato(Aminci ya tabbata a gareku da rahamar Allah da albarkarSa), banda musafahar da take faruwa alokacin farkon haɗuwa.
  4. Sallama addu'a ce, musulmai suna cikin buƙatuwar junansu su yi wa junansu addu'a koda hakan ya maimaitu.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 494) (5200). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص520). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 138). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 667). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 410).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN SALLAMA DA NEMAN IZINI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com