Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so

عَنْ أَبِي مَسْعُودٍ عُقْبَةَ بْنِ عَمْرٍو الأَنْصَارِيِّ البَدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ: «إِنَّ مِمَّا أَدْرَكَ النَّاسُ مِنْ كَلاَمِ النُّبُوَّةِ الأُولَى: إِذَا لَمْ تَسْتَحْيِ فَاصْنَعْ مَا شِئْتَ».
Daga Abu Mas'ud Uƙbah ibnu Amr al-Ansari al-Badri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa daga abinda ya zo a cikinsa wasicci game da Annabawa magabata, kuma mutane suka jujjuya shi tsakaninsu kuma suka gaje shi daga garesu ƙarni bayan ƙarni, har sai da yakai zuwa farkon wannan al'ummar, ka duba zuwa abinda kake son ka aikata shi, idan ya kasance abinda ba'a jin kunyarsa ne to ka aikata shi, idan ya kasance daga abinda ake jin kunyarsa ne to ka bar shi; domin abinda yake hana munanan ayyuka shi ne kunya, wanda ba shi da kunya, to sai ya kutsa a cikin kowace alfasha da abin ƙi.

Fa’idoji
  1. Kunya asalin manyan ɗabi'u ce.
  2. Kunya, siffa ce daga siffofin Annabawa - aminci ya tabbata agare su -, kuma ita tana daga abinda aka cirato daga garesu.
  3. Kunya ita ce wacce take sanya mutum musulmi ya aikata abinda zai sa shi kyau kuma ya ƙaway a shi, kuma ya bar abinda zai munana shi ya aibata shi.
  4. Nawawi ya ce: Umarni a cikinsa dan halacci ne, wato: Idan ka yi nufin aikata wani aiki idan ya kasance daga abinda baka jin kunyar Allah da ManzonSa ne idan ka aikata shi to ka aikata shi, inba haka ba to a'a (kada ka aikata) akan haka Musulunci yake, fuskantar hakan cewa abinda aka yi umarni da shi na wajibi ko na mandubi ana jin kunyar barinsa, abinda kuma aka hana na haram da makaruhi to ana jin kunyar aikata shi, amma abin da aka halatta aikata shi da barinsa to jin kunya a aikata shi ya halatta, haka nan a barinsa, sai hadisin ya ƙunshi hukunce-hukunce guda biyar. Akace: Shi umarni ne na tsawatarwa, kuma ma'anarsa: Idan an cire maka kunya to ka aikata abinda ka so; domin cewa Allah Mai yi maka sakayya ne akansa. An ce: Shi umarni ne a ma’anar labari, wato: Wanda ba ya jin kunya to ya aikata abinda ya so.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 29) (6120). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1252). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص1045). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 656).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com