Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu

عَنْ أَبِي يَعْلَى شَدَّادِ بْنِ أَوْسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ اللهَ كَتَبَ الْإِحْسَانَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ، فَإِذَا قَتَلْتُمْ فَأَحْسِنُوا القِتْلَةَ، وَإِذَا ذَبَحْتُمْ فَأَحْسِنُوا الذِّبْحَةَ، وَلْيُحِدَّ أَحَدُكُمْ شَفْرَتَهُ، وَلْيُرِحْ ذَبِيحَتَهُ».
Daga Abu Ya'ala Shaddadu ibnu Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu, idan zaku yi kisa to ku kyautata kisan, kuma idan zaku yi yanka to ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙar tasa, don ya hutar da abin yankansa»
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawar a kisa da yanka. Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe. Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.

Fa’idoji
  1. Rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarsa ga halitta.
  2. Kyautata kisa da yanka: shi ne ya kasance ta fuskar da shari'a ta halatta.
  3. Cikar shari'a da tattaruwarta a kan kowane alheri, yana daga cikin hakan jin ƙan dabbobi da tausasawa garesu.
  4. Hani daga musla ga mutum bayan kasheshi
  5. Haramta dukkanin abin da a cikinsa akwai azabtarwa ga dabbobi.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1548) (1955). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثا النووية (ص38). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص185). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص65). فتح الباري، لابن حجر (9/ 644). شرح النووي على مسلم (13/ 107).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
YANKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com