Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

YANKA

Hadisai 6

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu

عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: ضَحَّى النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِكَبْشَيْنِ أَمْلَحَيْنِ أَقْرَنَيْنِ، ذَبَحَهُمَا بِيَدِهِ، وَسَمَّى وَكَبَّرَ، وَوَضَعَ رِجْلَهُ عَلَى صِفَاحِهِمَا.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yanka raguna biyu wato mazan tumakai, masu fararen ƙahunhuna waɗanda baƙi ya cakuɗa da su, kuma ya ce: Da sunan Allah, Allah ne Mafi girma, kuma ya ɗora ƙafarsa akan wuyansu.

Fa’idoji
  1. Halaccin layya, haƙiƙa musulmai sun haɗu akanta.
  2. Abin da ya fi layya ta zama daga wannan nau'in da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da shi; dan kyan ganinsa da kuma kasancewar kitsensa da namansa yafi daɗi.
  3. AlNawawi ya ce: A cikinsa cewa an so mutum ya jiɓinci yanka layyarsa da kansa, kada ya wakilta a yankata sai da wani uzuri, a wannan lokacin an so ya halacci yankanta, idan ya wakilta wani musulmi ya halatta babu wani saɓani.
  4. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai son kabbara tare da basmala a lokacin yanka da son ɗora ƙafar dama akan fatar wuyan abin layyar, kuma sun haɗu akan cewa kwantar da ita yana kasancewa ne a ɓangaren hagu sai ya ɗora ƙafaresa akan ɓangaren dama dan ya zama ya fi sauƙi ga mai yankan a wurin riƙe wuƙa da dama, da riƙe kanta da hannunsa na hagu.
  5. An so layya da mai ƙaho kuma yana halatta da waninsa.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 102) (5565). صحيح مسلم (3/ 1556) (1966). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص724). الإعلام بفوائد عمدة الأحكام، لابن الملقن (10/ 179).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai akwai halayyar daji ga wadannan dabbobin kamar dabbobin daji, wanda ya bijere muku daga cikinsu to ku yi haka da shi'

عَنْ رَافِعِ بْنِ خَدِيجٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِذِي الحُلَيْفَةِ، فَأَصَابَ النَّاسَ جُوعٌ، فَأَصَابُوا إِبِلًا وَغَنَمًا، قَالَ: وَكَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي أُخْرَيَاتِ القَوْمِ، فَعَجِلُوا، وَذَبَحُوا، وَنَصَبُوا القُدُورَ، فَأَمَرَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِالقُدُورِ، فَأُكْفِئَتْ، ثُمَّ قَسَمَ، فَعَدَلَ عَشَرَةً مِنَ الغَنَمِ بِبَعِيرٍ فَنَدَّ مِنْهَا بَعِيرٌ، فَطَلَبُوهُ، فَأَعْيَاهُمْ وَكَانَ فِي القَوْمِ خَيْلٌ يَسِيرَةٌ، فَأَهْوَى رَجُلٌ مِنْهُمْ بِسَهْمٍ، فَحَبَسَهُ اللَّهُ، ثُمَّ قَالَ: «إِنَّ لِهَذِهِ البَهَائِمِ أَوَابِدَ كَأَوَابِدِ الوَحْشِ، فَمَا غَلَبَكُمْ مِنْهَا فَاصْنَعُوا بِهِ هَكَذَا»، فَقَالَ أي رافع: إِنَّا نَرْجُو -أَوْ نَخَافُ- العَدُوَّ غَدًا، وَلَيْسَتْ مَعَنَا مُدًى، أَفَنَذْبَحُ بِالقَصَبِ؟ قَالَ: «مَا أَنْهَرَ الدَّمَ، وَذُكِرَ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ فَكُلُوهُ، لَيْسَ السِّنَّ وَالظُّفُرَ، وَسَأُحَدِّثُكُمْ عَنْ ذَلِكَ: أَمَّا السِّنُّ فَعَظْمٌ، وَأَمَّا الظُّفُرُ فَمُدَى الحَبَشَةِ».
Daga rafi'u ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, sai suka samu raƙuma da tumakai, ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikin ƙarshen mutane, sai suka yi gaggawa, suka yanka, suka girka tukwane, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da tukwane, sai aka kifar da su, sannan ya raba, sai ya daidaita tumakai goma da raƙumi ɗaya sai wani raƙumi ya yi tsaurin kai, sai suka neme shi, sai ya gajiyar da su kuma a cikin mutanen dawakan kaɗan ne, sai wani mutum daga cikinsu ya sunkuyar da kibiya, sai Allah Ya tsare shi, sannan ya ce: "Lallai akwai halayyar daji ga wadannan dabbobin kamar dabbobin daji, wanda ya bijere muku daga cikinsu to ku yi haka da shi'. Sai ya ce: wato rafi'u: Lallai mu muna jin kwadayi - ko muna jin tsron - makiya gobe, kuma babu wuka a tare da mu, shin zamu yanka ne da kara? ya ce: "Duk abinda ya zubar da jini, kuma aka ambaci sunan Allah akansa to sai ku ci shi, banda hakori da farce, kuma zan zantar da ku game da haka: Amma a hakori to kashi ne, amma farce to wuƙar mutanen Habasha ce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Rafi'i ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-Hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, alhali sun samu ganimar raƙuma da tumakai daga mushrikai, sai suka yi gaggawa kafin raba ganima sai suka yanka wasu daga cikinsu, kuma suka kafa tukwane, ba tare da sun nemi izinin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba, kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a cikin ƙarshen mutane, lokacin da (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sani sai ya yi umarni da tukwanan, sai aka kifar da su da abinda ke cikinsu na miya, sannan ya raba ganimar a tsakaninsu, sai ya sanya goma daga cikin tumakai a madadin rakumi daya, sai wani rakumi ya gudu daga cikinsu, sai suka kasa kama shi, kuma dawakan sun kasance kada ne, sai wani mutum ya harbe shi da kibiya, sai Allah Ya tsare musu shi, sai (Annab) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai akwai wasu ɗabi'u kamar ɗabi'un daji ga waɗannan dabbobin masu sabo, wanda ya rinjayeku daga cikinsu kuma kuka kasa kama shi to ku yi haka da shi. Sai Rafi'u ya ce: Lallai mu mana fatan fuskantar maƙiya gobe, kuma muna jin tsoron yankanmu ga dabbobin ya cutar da makamanmu alhali ana tsananin buƙatar yanka, kuma babu wuƙa a tare da mu, shin zamu yanka ne da busassun karare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk abinda ya zubar da jini kuma ya kwaranyar da shi da yawa, kuma aka ambaci sunan Allah a kansa to ku ci shi, banda haƙori da farce, kuma zan zantar daku game da hakan: Amma haƙori to ƙashi ne, amma farce to mutanen Habsha kafirai ne suke amfani da shi.

Fa’idoji
  1. Bayyanar da wani ɓangare daga tawali'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda tafiyarsa a bayan runduna, da kuma kula da sahabbansa, da bibiyarsa garesu, da karɓar nasihar sahabbansa - Allah Ya yarda da su -.
  2. Ladabatarwar shugaba ga talakawansa da kuma rundunarsa, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ladabtar da su akan wannan gaggawar da kuma aikin da suka yi, kafin karɓar izninsa, sai sakamakonsu ya zama haramta musu abinda suka yi nufi.
  3. Gaggawar amsawar sahabbai - Allah Ya yarda da su - ga umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare su -.
  4. Hana ɗaukar ganima har sai an rabata.
  5. Adalci, musammanma agurin yaƙar maƙiya da kafirai; domin hakan yana daga sabubban nasara da rinjaye akan maƙiya.
  6. Nawawi ya ce: Idan dabbar gida ta koma mai ɗabi'ar ta daji shi ne raƙumi ko saniya ko doki su yi taurin kai ko akuya ta gudu ko waninsu to shi ya zama kamar farauta ne, sai ya halatta ta hanyar harbi.
  7. Yankan dabbobi yana wajaba dan cinsa ya halatta, dabbobi an sharɗanta musu abinda ke tafe: 1- Ya zama cinsa ya halatta. 2- Ya zama an samu iko a kansa, wanda ba'a samu iko a kansa ba to hukuncinsa shi ne hukuncin abin farauta. 3- Ya zama dabba ce ta sarari; amma dabbar ruwa to ba'a sharɗanta yanka gareta ba.
  8. Sharuɗɗan ingancin yanka: 1-Cancantar mai yankan shi ne ya zama mai hankali mai mayyazewa kuma musulmi ko mazuwa littafi (Bayahude ko Banasare). 2- Ya ambaci sunan Allah a farkon yankan. 3- Ingancin abin yankan ga yanka shi ne abin yankan da za’a yi amfani da shi ya zama mai kaifi cikin kowane irin abu ne banda haƙori da farce. 4- Yankan ya zama gurin da ake yankawane ko kuma sokewa a abinda ake da iko akansa ta hanyar yanke maɗaciya da maƙogwaro da jijiyoyi.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 138) (2488). صحيح مسلم (3/ 1558) (1968). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص721).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mun yi yanka a lokacin Annabi Doki kuma Muka ci namansa

عن أَسْمَاء بِنْت أَبِي بَكْرٍ رضي الله عنهما قالت: «نَحَرْنَا عَلَى عَهْدِ رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم فَرَسًا فَأَكَلْنَاهُ». وَفِي رِوَايَةٍ «وَنَحْنُ بِالْمَدِينَةِ».
Daga Asma'u Yar Abubakar ta ce: "Mun yi yanka a lokacin Annabi Doki kuma Muka ci namansa" a wata Riwayar kuma "Kuma Mu muna Madina".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana Asma'u tana Bada labarin cewa sun soke doki a lokacin Annabi kuma sun ci namansa, kuma cikin hakan akwai Dalilai kan Halaccin cin Naman doki kuma babu wanda zai kasa gane halacin hakan don kawai an hada ambatonsu da Jaki da Alfadari a ayar da take cewa: "Kuma doki da Alfadari da Jaki duk don ku haune kuma kuyi Ado kuma Allah yana halittar wasu Abubuwan da baku sani ba" [Annahl: 8].

Madogara

1- صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. 2- صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. 3- خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة: الثانية 1412هـ، 1992م. 4- الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ. 5- الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. 6- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، دار الميمان، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م. 7- تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، الطبعة: 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce ni da in tsaya a jikinsa, kuma in yi sadaka da namansu da fatarsu da kuma lokacinsu

عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه قال: «أَمَرَنِي رَسُول اللَّهِ -صلَّى الله عليه وسلَّم- أَن أَقُومَ عَلَى بُدْنِهِ، وَأَن أَتَصَدَّقَ بِلَحمِهَا وَجُلُودِهَا وَأَجِلَّتِهَا، وَأَن لا أُعْطِيَ الجَزَّارَ مِنهَا شَيْئًا».
Daga Aliyu bn Abi Talib - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce ni da in tsaya a jikinsa, kuma in yi sadaka da namansu da fatarsu da kuma lokacinsu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zo Makka a aikin hajji na bankwana kuma tare da shi wata kyauta, kuma Ali bin Abi Dalib - Allah ya yarda da shi - ya fito daga Yemen, kuma tare da shi kyauta, kuma tunda sadaka ce ga matalauta da mabukata, wanda ya ba ta ba shi da hakkin ya zubar da ita, ko wani abu daga cikin ta hanyar diyya. Ya hana shi ya ba ta yanka daga ita, a matsayin musanya na aikinsa, amma ya ba shi ladansa ban da namanta da fatanta kuma ya jinkirta

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu

عن شداد بن أوس رضي الله عنه قال: ثِنْتَانِ حَفِظْتُهُمَا عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ اللهَ كَتَبَ الْإِحْسَانَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ، فَإِذَا قَتَلْتُمْ فَأَحْسِنُوا الْقِتْلَةَ، وَإِذَا ذَبَحْتُمْ فَأَحْسِنُوا الذَّبْحَ، وَلْيُحِدَّ أَحَدُكُمْ شَفْرَتَهُ، فَلْيُرِحْ ذَبِيحَتَهُ».
Daga Shaddadu ɗan Aws - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Abubuwa guda biyu na haddacesu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu, idan za ku yi kisa, to, ku kyautata kisan, kuma idan za ku yi yanka, to, ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙarsa, ya hutar da abin yankansa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawar a kisa da yanka. Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe. Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.

Fa’idoji
  1. Rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarsa ga halitta.
  2. Kyautata kisa da yanka: shi ne ya kasance ta fuskar da shari'a ta halatta.
  3. Cikar shari'a da tattaruwarta a kan kowane alheri, yana daga cikin hakan jin ƙan dabbobi da tausasawa garesu.
  4. Hani daga musla ga mutum bayan kasheshi
  5. Haramta dukkanin abin da a cikinsa akwai azabtarwa ga dabbobi.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1548) (1955). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثا النووية (ص38). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص185). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص65). فتح الباري، لابن حجر (9/ 644). شرح النووي على مسلم (13/ 107).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu

عَنْ أَبِي يَعْلَى شَدَّادِ بْنِ أَوْسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ اللهَ كَتَبَ الْإِحْسَانَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ، فَإِذَا قَتَلْتُمْ فَأَحْسِنُوا القِتْلَةَ، وَإِذَا ذَبَحْتُمْ فَأَحْسِنُوا الذِّبْحَةَ، وَلْيُحِدَّ أَحَدُكُمْ شَفْرَتَهُ، وَلْيُرِحْ ذَبِيحَتَهُ».
Daga Abu Ya'ala Shaddadu ibnu Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu, idan zaku yi kisa to ku kyautata kisan, kuma idan zaku yi yanka to ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙar tasa, don ya hutar da abin yankansa»
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawar a kisa da yanka. Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe. Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.

Fa’idoji
  1. Rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarsa ga halitta.
  2. Kyautata kisa da yanka: shi ne ya kasance ta fuskar da shari'a ta halatta.
  3. Cikar shari'a da tattaruwarta a kan kowane alheri, yana daga cikin hakan jin ƙan dabbobi da tausasawa garesu.
  4. Hani daga musla ga mutum bayan kasheshi
  5. Haramta dukkanin abin da a cikinsa akwai azabtarwa ga dabbobi.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1548) (1955). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثا النووية (ص38). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص185). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص65). فتح الباري، لابن حجر (9/ 644). شرح النووي على مسلم (13/ 107).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com