Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa imani cikakke ba ya tabbata ga wani daga musulmai har sai ya so wa ɗan'uwansa abinda yake sowa kansa na ayyukan ɗa'a da nau'ukan alkairai a addini da rayuwa, kuma ya ki abinda yake ki ga kansa, idan ya ga wata tawaya ga ɗan'uwansa musulmi a addininsa, to ya yi kokari a cikin gyarata, idan ya ga wani alheri a cikinsa to ya daidaita shi ya taimake shi, ya yi masa nasiha a al'amarin Addininsa da duniyarsa.
- Wajabcin so wa mutum ga ɗan'uwansa abinda yake so wa kansa; domin kore imani ga wanda ba ya son abinda yake so ga ɗan'uwansa yana nuni akan wajabcin hakan.
- 'Yan uwantaka a tafarkin Allah sama take akan 'yan uwantaka ta nasaba, to hakkinta shi ne mafi wajaba.
- Haramcin dukkan abinda yake kore wannan soyayyar na maganganu da ayyuka, kamar algus da raɗa da hassada da ta'addanci akan ran musulmi ko dukiyarsa ko mutuncinsa.
- Yin anfani da wasu daga lafuzza masu kwaɗaitarwa akan yin aiki; saboda faɗinsa: "Ga ɗan'uwansa".
- Karmani - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Kuma yana daga cikin imani ya ki wa ɗan'uwansa abinda yake ki wa kansa na sharri, amma bai ambace shi ba; domin son abu mai lazimtar kin kishiyarsa ne , to hakan ya isu akan barin fadinsa.
صحيح البخاري (1/ 12) (13). صحيح مسلم (1/ 67) (45). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، مطبعة دار نشر الثقافة، الإسكندرية، الطبعة: الأولى، 1380 هـ. شرح الأربعين النووية، للشيخ ابن عثيمين، دار الثريا للنشر. فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، دار ابن القيم، الدمام المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى، 1424هـ/2003م. الفوائد المستنبطة من الأربعين النووية، للشيخ عبد الرحمن البراك، دار التوحيد للنشر، الرياض. الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله بن صالح المحسن، نشر: الجامعة الإسلامية، المدينة المنورة، الطبعة: الثالثة، 404هـ/1984م.