Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agate shi - ya bada labarin cewa kaɗai shi Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya aikoshi ne dan ya cika kyawawan ɗabi'u; inda aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cika abinda ya gabace shi na manzanni, kuma mai cika kyawawan ɗabi'un larabawa, sun kasance suna son alheri kuma suna ƙin sharri, masu mutunci ne da karamci da gabata; sai aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cike abubuwan da suka gaza da ke cikin ɗabi'unsu, kamar alfaharinsu da nasabobi, da girman kai, da wulaƙanta talaka da wanin hakan.
- Kwaɗaitarwa akan kyawawan ɗabi'u, da kuma hani daga kishiyoyinsu.
- Bayanin muhimmancin kyawawan ɗabi'u a cikin shari'ar Musulunci kuma cewa su suna daga abubuwan da ya baiwa kulawa gare su.
- Mutanen Jahiliyya sun kasance suna da ragowar kyawawan ɗabi'u, daga cikinsu akwai kyauta, da gwarzantaka, da wanin haka, sai Musulunci ya zo dan ya cikasu.
الأدب المفرد (ص104) (273). مسند أحمد (14/ 512) (8952). السنن الكبرى للبيهقي (10/ 191) (20819). عمدة القاري شرح صحيح البخاري (22/ 118).