Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَيْسَ الْمُؤْمِنُ بِالطَّعَّانِ وَلاَ اللَّعَّانِ وَلاَ الفَاحِشِ وَلاَ البَذِيءِ».
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba".
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bai zamo daga sha'anin mumimi mai cikakken imani ya zama mai yawan aibata mutane a cikin dangantakar su ba, kuma ba mai yawan zagi da tsinuwa bane, kuma ba mai yawan alfasha ne da aiki ko magana wacce babu kunya a cikinta ba.

Fa’idoji
  1. Kore imani a cikin nassosin shari'a ba ya kasancewa sai dan aikata wani aiki na haramun ko barin wajibi.
  2. Kwaɗaitarwa akan kiyaye gaɓɓai da kiyayesu daga munanan abubuwa, musamman ma harshe.
  3. Assindi ya ce: A cikin sigar mubalaga a cikin (mai yawan suka, da mai yawan tsinuwa) akwai nuni akan cewa idan suka da tsinuwa sun zama kadan ne ga wanda yake cancantar hakan ba ya cutarwa a cikin siffantuwa da siffofin ma'abota imani.
Madogara

سنن الترمذي (3/ 520) (1977)، تحفة الأحوذي (6/ 95)، مجموع الفتاوى (12/ 478).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com