Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare
عن عائشة رضي الله عنها قالت: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إنَّ المُؤْمِنَ ليُدرِكُ بِحُسْنِ خُلُقِهِ دَرَجَةَ الصَّائِمِ القَائِمِ».
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare.
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadDarajaIngantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana kyawawan ɗabi’u suna kai mai yin su matsayin mai azumi kullun da rana kuma mai Nafila da daddare, matattarar kyawawan ɗabi’u ita ce: bayar da kyakkyawan abu, da kyakkyawar magana, da sakin fuska da rashin cutar da mutane da jure cutarwarsu.
Fa’idoji
Girman yadda Musulunci ya kula da tsaftace kyawawan ɗabi’u da kuma cika su.
Falalar kyawawan ɗabi’u, har suna kai bawa ya samu matsayin mai azumi wanda ba ya hutawa, mai nafilar dare wanda ba ya gajiya.
Azumi da rana da Nafila da daddare ayyuka ne masu girma, suna da wahala ga rai, amma mai kyawawan ɗabi’u ya kai matsayinsu saboda ƙoƙari da ya yi a kansa da kyakkyawar mu’amala.
Madogara
سنن أبي داود (7/ 176) (4798).
مسند أحمد (40/ 414) (24355).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 675).
تطرز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص411).
مشكاة المصابيح، لمحمد العمري (3/ 1409).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com