Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba

عن جرير بن عبد الله رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ لَا يَرْحَمِ النَّاسَ لَا يَرْحَمْهُ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ».
Daga Jariri ɗan Abbdullah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda baya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba, to, jin ƙan bawa ga halitta yana daga mafi girman sabubban da ake samun rahamar Allah da su.

Fa’idoji
  1. Jin ƙai abin nema ne ga sauran ababen halitta, sai dai an keɓanci mutane da ambato ne don ba da muhimmanci garesu.
  2. Allah Shi ne Mai jin ƙai, kuma Yana jin ƙan bayinsa masu jin ƙai, to, sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki.
  3. Jin ƙai ga mutane ya tattaro alheri garesu da tunkuɗe sharri garesu da mu'amalantarsu da kykkyawa.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 10) (6013). صحيح مسلم (4/ 1809) (2319). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 553). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين (1/ 247). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 319).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com