Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa bawan da ya yi imani da Allah da ranar lahira wadda makomarsa take a cikinta, kuma a cikinta sakayyar aikinsa take, to, imaninsa zai kwaɗaitar da shi a kan aikata waɗannan ɗabi'un. Na farko: Magana mai kyau: Ta tasbihi da hailala, da horo da aikin alheri, da hani daga abin ƙi, da gyara a tsakaknin mutane, idan bai aikata ba, to, ya lazimci shiru, ya kame daga cutarwa, ya kiyaye harshensa. Na biyu: Girmama maƙoci: Da kyautata masa da rashin cutar da shi. Na uku: Girmama baƙo mai gabatowa don ziyararka: Ta hanyar daddaɗan zance da ciyar da abinci da makamancin hakan.
- Imani da Allah da ranar lahira asali ne ga kowane alheri, kuma yana zaburarwa a kan aikin alheri.
- Gargaɗi akan illolin harshe.
- Addinin musulunci addinin rangwa ne da karamci
- Waɗannan ɗabi'un suna daga yankin imani kuma daga ladubba ababen yabo.
- Yawaita zance zai iya kai wa zuwa abin ƙi ko abin haramtawa, kuɓuta tana cikin rashin magana sai ta alheri.
صحيح البخاري (8/ 11) (6018). صحيح مسلم (1/ 68) (47). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، (ص34). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص176). شرح النووي على مسلم (2/ 18).