Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska

عن أبي ذر رضي الله عنه قال: قال لي النبي صلى الله عليه وسلم: «لَا تَحْقِرَنَّ مِنَ الْمَعْرُوفِ شَيْئًا، وَلَوْ أَنْ تَلْقَى أَخَاكَ بِوَجْهٍ طَلْقٍ».
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce da ni: "Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya kwaɗaitar a kan aikin alheri, kuma kada ya wulaƙantashi ko da ya kasance kaɗan ne, daga wannan (akwai) sakin fuska ta hanyar murmushi a yayin haɗuwa, to, yana kamata ga musulmi ya yi kwaɗayi a kansa; saboda abin da ke cikinsa na ɗebe kewa ga ɗan uwa musulmi da shigar da farin ciki gareshi.

Fa’idoji
  1. Falalar soyayya a tsakanin muminai da murmushi da walwala a yayin haɗuwa.
  2. Cikar wannan shari'ar da tattarowarta, kuma ita ta zo da dukkanin abin da a cikinsa akwai gyara musulmai da haɗe kansu.
  3. Kwaɗaitarwa a kan aikata aikin alheri ko da ya ƙaranta.
  4. An so shigar da farin ciki ga musulmai; saboda abin da ke cikin hakan na tabbatar da sabo a tsakaninsu.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2026) (2626). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 119). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 341). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، (1/ 572). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 20).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com