Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa

عَنْ بَهْزِ بْنِ حَكِيمٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ قَالَ: قُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ: مَنْ أَبَرُّ؟ قَالَ: «أُمَّكَ، ثُمَّ أُمَّكَ، ثُمَّ أُمَّكَ، ثُمَّ أَبَاكَ، ثُمَّ الْأَقْرَبَ فَالْأَقْرَبَ».
Daga Bahzu ɗan Hakim daga babansa daga kakansa ya ce: Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa».
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mafi cancantar mutane da yi wa biyayya, da kyautata masa, da kyakkyawar mu'amala, da tsaftatacciyar mu'amala, da abokantakarsa da sadar da zumuncinsa: Ita ce uwa, kuma ya ƙarfafa haƙƙin uwa akan waninta da maimaitawarsa sau uku; dan bayanin falalarta akan ragowar mutane ba tare da togancewa ba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai bayyana wanda yake biye mata a biyayya: Sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci daga 'yan dangi, kuma a duk lokacin da ya zama ya fi kusanci to ya zama mafi cancanta da sadar da zumunci daga mafi nesa.

Fa’idoji
  1. A cikin hadisin akwai gabatar da uwa, sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci, gwarwadan darajojinsu a kusanci.
  2. Bayanin matsayin mahaifa musamman uwa.
  3. A cikin hadisin ya maimaita yi wa uwa biyayya sau uku; hakan dan girman falalarta akan 'ya'yanta, da kuma yawan abinda take ɗauka na wahalhalu da gajiya da kuma wahalar ciki, sannan haihuwa, sannan shayarwa, abubwan da uwa take kaɗaitaka da shi, sannan ta yi tarayya da uba a cikin tarbiyya.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 453) (5139). سنن الترمذي (3/ 463) (1897). مسند أحمد (33/ 230) (20028). عون المعبود شرح سنن أبي داود، للعظيم آبادي (14/ 33). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (6/ 54). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 187). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 194).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN BIN IYAYE

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com