Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba

عَنْ أُمِّ عَطِيَّةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: نُهِينَا عَنِ اتِّبَاعِ الجَنَائِزِ، وَلَمْ يُعْزَمْ عَلَيْنَا.
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ummu Aɗiyya al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata bin jana'iza; hakan saboda abinda ake jin tsoro a cikin hakan na fitina garesu da kuma fitinuwa da su, da kuma ƙarancin haƙurinsu, sannan Allah Ya yarda da ita ta bada labarin cewa bai ƙarfafa hanin ba kamar yadda yake aikatawa a sauran abubuwan da ya hana.

Fa’idoji
  1. Hana mata bin jana'iza, kuma hakan mai gamewa ne a binta zuwa inda ake shirya gawar da kuma yi mata sallah, da kuma zuwa maƙabarta inda za'a rufeta.
  2. dalilin hanin shi ne mata ba sa iya ganin irin waɗannan guraren masu baƙanta rai da kuma abubuwa masu tasiri; wataƙila fishi da rashin haƙuri akan abinda zai kore haƙuri na wajibi ya bayyana daga garesu.
  3. Asali a cikin hanin shi ne haramci, saidai cewa Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta fahimta ta hanyar alamar hali cewa hanasu bin jana'izar da aka yi ba a yanke yake ba, kuma ba mai ƙarfi ba ne, saidai haƙiƙa wasu hadisan sun zo mafi yawa daga abinda suke nuni akan tsananin bin jana'iza sama daga abinda wannan hadisin yake nuni a kansa.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 78) (1278). صحيح مسلم (2/ 646) (938). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص285). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 366).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ABUBUWAN DA LAFAZAI SUKE NUNAWA DA YADDA AKE FITAR DA HUKUNCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com