Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ABUBUWAN DA LAFAZAI SUKE NUNAWA DA YADDA AKE FITAR DA HUKUNCI

Hadisai 3

An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba

عَنْ أُمِّ عَطِيَّةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: نُهِينَا عَنِ اتِّبَاعِ الجَنَائِزِ، وَلَمْ يُعْزَمْ عَلَيْنَا.
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ummu Aɗiyya al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata bin jana'iza; hakan saboda abinda ake jin tsoro a cikin hakan na fitina garesu da kuma fitinuwa da su, da kuma ƙarancin haƙurinsu, sannan Allah Ya yarda da ita ta bada labarin cewa bai ƙarfafa hanin ba kamar yadda yake aikatawa a sauran abubuwan da ya hana.

Fa’idoji
  1. Hana mata bin jana'iza, kuma hakan mai gamewa ne a binta zuwa inda ake shirya gawar da kuma yi mata sallah, da kuma zuwa maƙabarta inda za'a rufeta.
  2. dalilin hanin shi ne mata ba sa iya ganin irin waɗannan guraren masu baƙanta rai da kuma abubuwa masu tasiri; wataƙila fishi da rashin haƙuri akan abinda zai kore haƙuri na wajibi ya bayyana daga garesu.
  3. Asali a cikin hanin shi ne haramci, saidai cewa Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta fahimta ta hanyar alamar hali cewa hanasu bin jana'izar da aka yi ba a yanke yake ba, kuma ba mai ƙarfi ba ne, saidai haƙiƙa wasu hadisan sun zo mafi yawa daga abinda suke nuni akan tsananin bin jana'iza sama daga abinda wannan hadisin yake nuni a kansa.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 78) (1278). صحيح مسلم (2/ 646) (938). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص285). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 366).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «دَعُونِي مَا تَرَكْتُكُمْ، إِنَّمَا هَلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ بِسُؤَالِهِمْ وَاخْتِلَافِهِمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ، فَإِذَا نَهَيْتُكُمْ عَنْ شَيْءٍ فَاجْتَنِبُوهُ، وَإِذَا أَمَرْتُكُمْ بِأَمْرٍ فَأْتُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu, idan na haneku daga wani abu to ku nuisance shi, idan na umarceku da wani abu to ku zo da shi daidai ikonku".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa hukunce-hukuncen shari'a sun rabu gida uku: Abinda aka yi shiru akan sa, da abubuwan da aka hana, da abubuwan da aka yi umarni. Amma na farko: Shi ne wanda shari'a ta yi shiru akansa, ta yadda babu wani hukunci, sai kuma cewa asali a abubuwa rashin wajabci; amma a zamaninsa - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - to barin tambaya ga wani abu da bai afku ba yana wajaba dan tsoron kada a wajabta ko haramci ya sauka a kan shi, domin Allah Ya bar su ne dan rahama ga bayi. Amma bayan rasuwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan tambayar ta kasance ta fuskar neman fatawa ce ko koyarwa ga abinda ake buƙatuwa a gare shi na al'amarin addini to ya halatta, kai an yi umarni da shi ma, idan kuma ta fuskar ta'annututi ce da ɗorawa kai to shi ne abinda ake nufi da barin tambaya daga gare shi a cikin wannan Hadisin; hakan domin cewa shi zai iya kaiwa zuwa kwatankwacin abinda ya afku ga Banu Isra'ila, dan an umarce su su yanka saniya da sun yanka kowacce irin saniya da sun aikata umarni, sai dai su sun tsananta sai aka tsananta musu. Na biyu: Abubuwan da aka hana; su ne: Abinda ake bawa wanda ya bar shi lada, kuma ana yi wa wanda ya aikata shi uƙuba, to nisantarsu yana wajaba. Na uku: Abubuwan da aka umarta; shi ne abinda ake bawa wanda ya aikata shi lada, kuma ana yi wa wanda ya bar shi uƙuba, to yana wajaba ya aikata shi gwargwadan iko.

Fa’idoji
  1. Abinda ya kamata a shagalta da mafi muhimmancin abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi, da barin abin da ba'a buƙatuwa zuwa gare shi a wannan lokaci, da barin shagaltuwa da tambaya daga abinda bai afku ba.
  2. Haramcin tambayar da wataƙila ta kai zuwa ƙulle mas'aloli, da buɗe ƙofar shubuhohi masu kaiwa zuwa yawan saɓani.
  3. Umarni da barin dukkan abinda aka hana; domin babu wata wahala a barinsu, saboda haka hanin da aka ya yi zama gamamme.
  4. Umarni da aikata abinda aka yi umarni da shi gwargwadan iko; domin zai iya lizimtar da wahala ko a gajiya a aikata shi; saboda haka umarni da shi ya zama akan gwargwadan iko.
  5. Hani akan yawan tambaya, haƙiƙa malamai sun raba tambaya gida biyu: Ta ɗayansu: Wadda take kasancewa ta fuskar koyarwa ga abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi na al'amarin addini, to wannan an yi umarni da ita, daga wannan nau'in tambayoyin sahabbai suke. Na biyu: Wadda ta kasance ta fuskar ta'annuti da ɗorawa kai to wannan ita ce wacce aka hana.
  6. Gargaɗin wannan al'ummar daga saɓawa annabinta, kamar yadda ya afku a cikin al’ummun da suka gabata.
  7. Yawan tambaya yana daga abinda ba'a buƙatuwa zuwa gare shi, kuma saɓawa annabawa sababi ne na halaka, musamman ma a cikin al'amuran da kaiwa gare su ba zai yi wu ba, misalin: Mas'alolin gaibun da babu wanda ya sansu sai Allah, da halayen ranar Alkiyama.
  8. Hana yin tambaya a mas'aloli masu tsanani, Auza'i ya ce: Lallai Allah idan Ya yi nufin haramtawa bawanSa albarkar ilimi sai Ya jefawa harshensa galaɗi mai yawa, haƙiƙa na gansu (sune) mafi ƙarancin mutane a ilimi. Ibnu Wahab ya ce: Na ji Malik yana cewa: Gaddama a cikin ilimi tana tafiyar da hasken ilimi daga zuciyar mutum.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 94) (7288). صحيح مسلم (2/ 975) (1337). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 236). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 181). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 268).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu.

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «ما نهيتكم عنه فاجتنبوه، وما أمرتكم به فأْتُوا منه ما استطعتم، فإنما أَهلَكَ الذين من قبلكم كثرةُ مسائلهم واختلافهم على أنبيائهم».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi: "Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah -Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana nuna mana cewa shi idan ya hanamu wani abu ya wajaba akanmu mu nisance shi ba tare da wata togaciya ba, kuma idan ya Umarcemu da wani abu kan mu yi shi to muyi gwargwadon iko sannan ya tsawatar mana don kada mu zamanto irin wasu Al'ummai da suka gabata lokacin da suka yawaita tambayoyi ga Annabawansu kuma suka saba musu sai Allah yayi musu Ukuba da Nau'o'in Hallaka da rusawa to ya dace kada mu kasance irin su don kada mu hallaka kamar yada suka hallaka.

Madogara

-التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، مطبعة دار نشر الثقافة، الإسكندرية، الطبعة: الأولى، 1380 هـ. -شرح الأربعين النووية، للشيخ ابن عثيمين، دار الثريا للنشر. -فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، دار ابن القيم، الدمام المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى، 1424هـ/2003م. -الفوائد المستنبطة من الأربعين النووية، للشيخ عبد الرحمن البراك، دار التوحيد للنشر، الرياض. -شرح الأربعين النووية، للشيخ صالح آل الشيخ، دار الحجاز، الطبعة: الثانية، 1433هـ. -الأربعون النووية وتتمتها رواية ودراية، للشيخ خالد الدبيخي، ط. مدار الوطن. -الجامع في شروح الأربعين النووية، للشيخ محمد يسري، ط. دار اليسر. -صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. -صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com