Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهُما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم: نَهَى عَنْ كُلِّ ذِي نَابٍ مِنَ السِّبَاعِ، وَعَنْ كُلِّ ذِي مِخْلَبٍ مِنَ الطَّيْرِ.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga cin dukkan zakuna daga dabbobin masu farauta waɗanda suke farauta ta hanyar hakoransu, da kuma cin dukkan tsuntsun da yake yankewa kuma yake kamu da faratansa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗayin musulunci akan abubuwa tsarkaka na halas a cikin kowane abu daga abubuwan ci da abubuwan sha da wasunsu.
  2. Asali, a cikin abubuwan ci shi ne halacci; sai abinda dalili ya yi nuni akan haramcinsa.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1534) (1934). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 506). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 5). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 6). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (9/ 173). فتاوى اللجنة الدائمة - المجموعة الأولى (22/ 290).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ABIN DA YA HALATTA DAGA CIKIN DABBOBI DA TSUNTSAYE

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com