Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ABIN DA YA HALATTA DAGA CIKIN DABBOBI DA TSUNTSAYE

Hadisai 8

Mun ta so Zomo a kwarin Zahran sai Mutane suka bishi a guje sai suka ka kasa

عن أنس رضي الله عنه قال: «أَنْفَجْنَا أَرْنَباً بِمَرِّ الظَّهْرَانِ، فَسَعَى الْقَوْمُ فَلَغَبُوا، وَأَدْرَكْتُهَا فَأَخَذْتُهَا، فَأَتَيْتُ بِهَا أَبَا طَلْحَةَ، فَذَبَحَهَا وَبَعَثَ إلَى رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم بِوَرِكِهَا وَفَخِذَيْهَا فَقَبِلَهُ».
Daga Anas -Allah ya yada da shi- ya ce: "Mun ta so Zomo a kwarin Zahran sai Mutane suka bishi a guje sai suka ka kasa, sai na na cimmasa sai na kama shi, sai na zo da shi wajen Abu Xalha sai ya yanka shi kuma ya aikawa da Manzon Allah SAW da cinyarsa kuma ya karva"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار علماء السلف، الطبعة: الثانية 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mun kasance tare da Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- sai ya ce akawo masa Daron abinci, cikinsa akawai Naman Kaza

عن زَهْدَم بن مُضَرِّبٍ الْجَرْمي قالَ: «كنا عند أبي موسى الأشعري، فدعا بمائدة وعليها لحم دجاج، فدخل رجل من بني تَيْمِ الله أَحْمَرُ، شَبِيهٌ بِالمَوَالِي، فقال له: هَلُمَّ، فَتَلَكَّأَ، فقال له: هَلُمَّ، فإني رأيتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم يأكل منه».
Daga Zahdam Bn Muxrib Al-Jarmi ya ce: "Mun kasance tare da Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- sai ya ce akawo masa Daron abinci, cikinsa akawai Naman Kaza, sai wani Mutum Ja daga cikin Bani taimillahi ya zo, yayi kama da bayi, sai yace taho mu ci, sai Mutumin yaqi, sai yace da shi taho mu ci saboda naga manzon Allah SAW yana cin kaza"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Daga Zahdam Bn Muxrib Al-Jarmi ya ce: "Mun kasance tare da Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- sai ya ce akawo masa Daron abinci, cikinsa akawai Naman Kaza, sai wani Mutum Ja daga cikin Bani taimillahi ya zo, yayi kama da bayi, sai yace taho mu ci, sai Mutumin yaqi, sai yace da shi taho mu ci saboda naga manzon Allah SAW yana cin kaza"

Madogara

-صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. -صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ. -عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ. -تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. -تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Munyi yaki tare da Manzon Allah Yakuna guda bakwai, muna ta cin Fara

عن عَبْد اللهِ بن أبي أوفى رضي الله عنهما قال: «غَزَوْنَا مَعَ رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم سَبْعَ غَزَوَاتٍ، نَأْكُلُ الْجَرَادَ».
Daga Abdullahi Dan Abi wakkas ya ce: "Munyi yaki tare da Manzon Allah Yakuna guda bakwai, muna ta cin Fara"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Cewa A;llah shi ne wanda ya Azurta Sahabbai da Yakuna bakwai kuma kare su da fara sabida rashin abinci a gurinsu, kamar yadda ya kare su da Babban kifin Anbar wanda ya futo daga kogi suka ci daga shi a wani yakin.

Madogara

- صحيح البخاري، دار طوق النجاة، ط 1422هـ. - صحيح مسلم، ط دار إحياء التراث العربي، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي. - خلاصة الكلام، فيصل آل مبارك ط. الثانية 1412هـ. - الإفهام لابن باز، ط مؤسسة الجريسي تحقيق سعيد القحطاني. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام، ط. دار الميمان، 1426هـ. - تأسيس الأحكام للنجمي، ط دار المنهاج، 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mun yi yanka a lokacin Annabi Doki kuma Muka ci namansa

عن أَسْمَاء بِنْت أَبِي بَكْرٍ رضي الله عنهما قالت: «نَحَرْنَا عَلَى عَهْدِ رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم فَرَسًا فَأَكَلْنَاهُ». وَفِي رِوَايَةٍ «وَنَحْنُ بِالْمَدِينَةِ».
Daga Asma'u Yar Abubakar ta ce: "Mun yi yanka a lokacin Annabi Doki kuma Muka ci namansa" a wata Riwayar kuma "Kuma Mu muna Madina".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana Asma'u tana Bada labarin cewa sun soke doki a lokacin Annabi kuma sun ci namansa, kuma cikin hakan akwai Dalilai kan Halaccin cin Naman doki kuma babu wanda zai kasa gane halacin hakan don kawai an hada ambatonsu da Jaki da Alfadari a ayar da take cewa: "Kuma doki da Alfadari da Jaki duk don ku haune kuma kuyi Ado kuma Allah yana halittar wasu Abubuwan da baku sani ba" [Annahl: 8].

Madogara

1- صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. 2- صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. 3- خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة: الثانية 1412هـ، 1992م. 4- الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ. 5- الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. 6- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، دار الميمان، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م. 7- تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، الطبعة: 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ عَامَ الفَتْحِ وَهُوَ بِمَكَّةَ: «إِنَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ حَرَّمَ بَيْعَ الخَمْرِ، وَالمَيْتَةِ وَالخِنْزِيرِ وَالأَصْنَامِ»، فَقِيلَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَرَأَيْتَ شُحُومَ المَيْتَةِ، فَإِنَّهَا يُطْلَى بِهَا السُّفُنُ، وَيُدْهَنُ بِهَا الجُلُودُ، وَيَسْتَصْبِحُ بِهَا النَّاسُ؟ فَقَالَ: «لاَ، هُوَ حَرَامٌ»، ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عِنْدَ ذَلِكَ: «قَاتَلَ اللَّهُ اليَهُودَ إِنَّ اللَّهَ لَمَّا حَرَّمَ شُحُومَهَا جَمَلُوهُ، ثُمَّ بَاعُوهُ، فَأَكَلُوا ثَمَنَهُ».
Daga Jabir ɗan Abdullah - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, yana faɗa a shekarar buɗe Makka alhali shi yana Makkah: "Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka", sai aka ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin kitsen mushe, cewa su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma ana shafe fatu da su, kuma mutane suna fitila da su? sai ya ce: "A'a, shi haramun ne", sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a wannan lokacin: "Allah Ya la'anci Yahudawa lallai Allah yayin da Ya haramta kitsensu sai suka gyara shi, sannan suka saida shi, sai suka ci kuɗinsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda ad shi - ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa a shekarar da aka buɗe Makka, alhali shi yana Makka: Lallai Allah da ManzonSa sun haramta saida giya da mushe da alade da gumaka, sai aka ce : Ya Manzon Allah, shin ya halatta mu saida kitsen mushe? domin su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma shafe fatu da su, kuma mutane suna kunna fitilunsu da su, sai ya ce: A'a, saida su haramun ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce a wannan lokacin: Allah Ya halakar da Yahudawa kuma Ya la'ancesu; lallai Allah yayin da Ya haramta musu kitsen dabbobi sai suka narkasu, sannan suka saida mansu suka ci kuɗinsa.

Fa’idoji
  1. AlNawawi ya ce: Mushe da giya da alade: Musulmai sun haɗu akan haramcin saida kowanne ɗaya daga cikinsu.
  2. Alƙali ya ce: Wannan Hadisin ya ƙunshi cewa abinda cinsa da anfani da shi ba ya halatta to saida shi ba ya halatta, kuma cin kuɗinsa ba ya halatta, kamar yadda yake a cikin kitsen da aka anbata a cikin Hadisin.
  3. Ibnu Hajar ya ce: Siyaƙin mai alamtarwa ne da ƙarfin dalili akan abinda mafi yawa suka yi tawilinsa cewa abin nufi da faɗinsa: "Shi haramun ne'’, siyarwa ba anfani ba.
  4. Dukkan dabarar da za'a kai ga halatta haram da ita to ita ɓatacciya ce.
  5. Nawawi ya ce: Malamai su ce: A cikin gamewar haramcin saida mushe cewa saida jikin kafiri yana haramta idan mun kashe shi, kuma kafirai suka nemi siyansa, ko bada canjinsa daga gare shi, haƙiƙa ya zo a cikin Hadisi: Cewa Naufal ɗan Abdulahi AlMakhzumi musulmai sun kashe shi ranar Khandaƙ, sai kafirai suka bada dirhami dubu goma ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga jikinsa bai karɓa ba, ya ba su shi.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 84) (2236). صحيح مسلم (3/ 1207) (1581). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، (ص97). فتاوى اللجنة الدائمة - المجموعة الأولى- اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء (22/ 506). الشرح الممتع على زاد المستقنع، لابن عثيمين (1/ 71). كشف اللثام شرح عمدة الأحكام، لمحمد السفاريني الحنبلي (4/ 557). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص479).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An halatta muku Matattu guda biyu da jini guda biyu, amma Matattun sune Kifi da Fara, kuma Jinin shi ne Zuciya da Hanta

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «أُحِلَّتْ لكم مَيْتَتَانِ وَدَمَانِ، فأما الميتتان: فَالْجَرَادُ والْحُوتُ، وأما الدَّمَانِ: فالكبد والطحال».
Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "An halatta muku Matattu guda biyu da jini guda biyu, amma Matattun sune Kifi da Fara, kuma Jinin shi ne Zuciya da Hanta"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

1. توضيح الأحكام للشيخ البسام، ط5، مكتبة الأسدي، مكة المكرمة، 1423ه. 2. سُبل السلام، للصنعاني، دار الحديث. 3. تسهيل الإلمام، للشيخ صالح الفوزان، بعناية: عبدالسلام السليمان، ط1، 1427ه. 4. شرح الشيخ ابن عثيمين للبلوغ، تحقيق صبحي رمضان وآخر، ط1، المكتبة الإسلامية، مصر، 1427ه. 5. منحة العلَّام للشيخ عبد الله بن صالح الفوزان، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1427ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Umarni da a Kashe Tsaka kuma ya ce: ta kasance tana busa ga Annabi ibrahim

عن أم شريك رضي الله عنها : أن رسول الله صلى الله عليه وسلم أمرها بِقَتْلِ الأَوْزَاغِ وقال: «كان يَنْفُخُ على إبراهيم».
Daga Ummu Shuraik -Allah ya yarda da ita- Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Umarni da a Kashe Tsaka kuma ya ce: ta kasance tana busa ga Annabi ibrahim"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، دار الكتاب العربي-بيروت. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشرة، 1407هـ. - مرقاة المفاتيح :علي بن سلطان القاري -دار الفكر، بيروت - لبنان الطبعة الأولى، 1422هـ - 2002م. - شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ. - فيض القدير شرح الجامع الصغير، زين الدين عبد الرؤوف المناوي القاهري -المكتبة التجارية الكبرى – مصر-الطبعة: الأولى، 1356هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهُما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم: نَهَى عَنْ كُلِّ ذِي نَابٍ مِنَ السِّبَاعِ، وَعَنْ كُلِّ ذِي مِخْلَبٍ مِنَ الطَّيْرِ.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga cin dukkan zakuna daga dabbobin masu farauta waɗanda suke farauta ta hanyar hakoransu, da kuma cin dukkan tsuntsun da yake yankewa kuma yake kamu da faratansa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗayin musulunci akan abubuwa tsarkaka na halas a cikin kowane abu daga abubuwan ci da abubuwan sha da wasunsu.
  2. Asali, a cikin abubuwan ci shi ne halacci; sai abinda dalili ya yi nuni akan haramcinsa.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1534) (1934). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 506). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 5). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 6). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (9/ 173). فتاوى اللجنة الدائمة - المجموعة الأولى (22/ 290).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com