Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani musulmin da zai ziyarci wani musulmi a cikin rashin lafiyarsa wanda lokacin mutuwarsa bai yi ba, sannan mai ziyarar ya yi wa mara lafiya addu'a da faɗinsa: (Ina roƙon Allah Mai girma) a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, (Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya), kuma ya maimaitata hakan sau bakwai sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar.
Fa’idoji
An so addu'a ga mara lafiya da wannan addu'ar, da kuma maimaitata sau bakwai.
Tabbatar da waraka ga wanda aka faɗi wannan addu'ar a wurinsa da izinin Allah - Maɗaukakin sarki -, in ta bijiro da gaskiya da kuma salaha.
Zai faɗi wannan addu'ar ne a ɓoye da bayyane, dukkan hakan ya halatta, sai dai idan ya jiyar da mara lafiyar to shi ya fi; domin a cikinsa akwai shigar da farin ciki gare shi.
Madogara
سنن أبي داود (5/ 22) (3106).
سنن الترمذي (3/ 593) (2083).
السنن الكبرى للنسائي (9/ 385) (10820).
مسند أحمد (4/ 40) (2137).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 163).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص537).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 483).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (11/ 559).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 689).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com