عن حُصين بن عبد الرحمن قال: كنتُ عند سعيد بن جُبير فقال: أيكم رأى الكوكب الذي انقَضَّ البارحة؟ فقلتُ: أنا، ثم قلتُ: أما إني لم أكن في صلاة، ولكني لُدغْتُ، قال: فما صنعتَ؟ قلت: ارتقيتُ، قال: فما حَمَلك على ذلك؟ قلت: حديث حدَّثَناه الشعبي، قال: وما حدَّثَكم؟ قلتُ حدثنا عن بريدة بن الحُصيب أنه قال: "لا رُقْية إلا مِن عَيْن أو حُمَة"، قال: قد أحسَن مَن انتهى إلى ما سمع، ولكن حدثنا ابن عباس عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال:
"عُرضت عليّ الأُمم، فرأيتُ النبي ومعه الرَّهط والنبي ومعه الرجل والرجلان، والنبي وليس معه أحد، إذ رُفع لي سواد عظيم فظننتُ أنهم أمَّتي، فقيل لي: هذا موسى وقومه، فنظرتُ فإذا سواد عظيم، فقيل لي: هذه أمَّتك، ومعهم سبعون ألفا يدخلون الجنة بغير حساب ولا عذاب، ثم نهض فدخل منْزله، فخاض الناس في أولئك؛ فقال بعضهم: فلعلهم الذين صحِبوا رسول الله صلى الله عليه وسلم وقال بعضهم: فلعلهم الذين وُلِدُوا في الإسلام فلم يشركوا بالله شيئا، وذكروا أشياء، فخرج عليهم رسول الله صلى الله عليه وسلم فأخبروه، فقال: هم الذين لا يَسْتَرقون، ولا يَكْتَوُون، ولا يَتَطَيَّرون، وعلى ربهم يتوكلون، فقام عُكاشة بن مِحصَن فقال: ادع الله أن يجعلني منهم، قال: أنت منهم، ثم قام جل آخر فقال: ادع الله أن يجعلني منهم، فقال: سَبَقَك بها عكاشة".
Daga Husayn bn Abd al-Rahman, ya ce: Na kasance tare da Sa'eed bin Jubair sai ya ce: Wanene a cikinku ya ga duniyar da ta share jiya? Na ce: Ni ne, sai na ce: Amma ni ba na cikin sallah, amma an yi min duri, ya ce: Me ka yi? Na ce: Na tashi, ya ce: Me ya sanya ka jure a kan haka? Na ce: Hadisi ne da muka ba da labari ga al-Sha`bi. Na ce: Ka fada mana a kan Buraydah bin Al-Husayb cewa ya ce: “Babu ruqyah sai daga ido ko suruka.” Ya ce: Wanda ya gama ya yi kyau ga abin da ya ji. Annabi yana tare da shi da annabi, kuma tare da shi mutum da mutanen biyu, da annabi kuma babu wani a tare da shi, yayin da aka kawo min bakar fata mai girma, kuma na zaci cewa su al'ummata ne, sai aka ce min: wannan shi ne musa da mutanensa. Sannan ya tashi ya shiga gidansa, kuma mutane suka yi fada a cikin wadancan. Don haka sai suka gaya masa, sannan ya ce: Su ne wadanda ba sa bautar, ba sa buya, kuma su tashi, kuma Ubangijinsu ya dogara gare su, don haka Okasha bin Mohsen ya tashi ya ce: Ina rokon Allah ya sanya ni a cikinsu, sai ya ce: Kai kana cikinsu, sai wani zamani ya tashi ya ce: Ina rokon Allah ya sanya ni daga cikinsu. Okasha sun riga ka. "
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
-صحيح البخاري، المحقق: محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه.
-صحيح مسلم، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.
-الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة، الرياض، الطبعة: الأولى، 1422ه - 2001م.
-الجديد في شرح كتاب التوحيد، مكتبة السوادي، جدة، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الخامسة، 1424هـ - 2003م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إنَّ الرُّقَى والتَمائِمَ والتِّوَلَةَ شِرْكٌ».
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana wasu abubuwa (waɗanda) aikatasu yana daga shirka; daga cikinsu akwai:
Na ɗaya: Tawaida: Zancen da 'yan Jahiliyya suke neman waraka da shi wanda ya haɗo shirka.
Na biyu: Layu na tsarkiya da makamancinta: Waɗanda ake ratayawa yara da dabbobi da wasunsu dan tunkuɗe kambun baka.
Na uku: Tiwala: Wacce akeyi don jawo soyayyar ɗaya daga cikin ma'aurata zuwa ɗayan.
Waɗannan al'amuran suna daga shirka; domin suna daga cikin riƙar abu a matsayin sababi, kuma shi ba sababi ne na shari'a ba wanda ya tabbata da dalili, ba kuma sababi ne na zahiri ba da ya tabbata da gwadawa. Amma sabubba na shari'a kamar karanta Al-ƙur'ani, ko na zahiri kamar magunguna da suka tabbata ta hanyar gwadawa, to, su sun halatta tare da ƙudire cewa su sabubba ne, kuma amfani da cuta suna hannun Allah ne.
Fa’idoji
- Kiyaye tauhidi da aƙida daga abin da yake ɓata su.
- Haramta yin amfani tawaida ta shirka da layu da tiwala.
- Ƙudirewar mutum a waɗannan abubuwa ukun cewa su sabubba ne: Shi ne shirka ƙarama; domin ya sanya abin da ba sababi ba ne a matsayin sababi, amma idan ya ƙudire cewa suna amfanarwa kuma suna cutarwa a kan kansu, to, shi shirka ne babba.
- Gargaɗi a kan aikata sabubba na shirka da kuma ababen haramtawa.
- Haramta (nau'o'in) tawaida kuma suna daga shirka, sai dai abin da aka shara'anta daga cikinsu.
- Ya kamata a rataya zuciya ga Allah Shi kaɗai, cuta da amfani daga gareshi ne Shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkuɗe sharri sai Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Tawaida da ta halatta ita ce wacce ta tattaro sharuɗɗa uku; 1- Ya ƙudire cewa su sababi ne ba sa amfanarwa sai da izinin Allah. 2- Ta kasance da Al-ƙur'ani da kuma sunayen Allah da siffofinSa da addu'o'in Annabi da wasu ababen shara'antawa. 3- Ta zama da yare abin fahimta, kuma kada ta ƙunshi ɗalasimai (saƙandamai) da sha'awazah (surkulle).
Madogara
سنن أبي داود (6/ 31) (3883).
سنن ابن ماجه (4/ 554) (3530).
مسند أحمد (6/ 110) (3615).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص91).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص79).
القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 180).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا أَتَى الْمَرِيضَ يَدْعُو لَهُ قَالَ: «أَذْهِبِ الْبَاسَ، رَبَّ النَّاسِ، وَاشْفِ أَنْتَ الشَّافِي، لَا شِفَاءَ إِلَّا شِفَاؤُكَ، شِفَاءً لَا يُغَادِرُ سَقَمًا».
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wajan mara lafiya yana yi masa addu'a zai ce : «Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ziyarci wani mara lafiya zai yi masa addu'a sai ya ce: Ya Allah (Ka tafiyar) Ka gusar da (tsanani) da tsananin rashin lafiya, (ya Ubangijin mutane) kuma Mahaliccinsu kuma Mai renansu, (Ka warkar da) wannan mara lafiyar (Kai ne) tsarki ya tabbatar maKa (Mai warkarwa) ina kamun ƙafa zuwa gareKa da sunanKa Mai warkarwa, (babu wata waraka) mai tabbata ga mara lafiya (sai warakarKa) da kuma lafiyarKa, (waraka) kai tsaye (wacce bata bari) ta wanzar ta kuma bar (wata masassara) da wani rashin lafiyar daban.
Fa’idoji
- Mai warkarwa Shi ne Allah - Mai girma da ɗaukaka -, amma likita da magani to su biyun sabubba ne basa anfanarwa kuma ba sa cutarwa sai da izinin Allah.
- Gaida mara lafiya yana daga haƙƙoƙi tsakanin musulmai, hakan cancanta ga iyalai.
- Kwaɗaitarwa ga wanda ya ziyarci mara lafiya ya yi masa wannan addu'ar mai albarka waccea aka ruwaito.
- Daga shiryrwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yin magani da ruƙya ta shari'a da Alƙur'ani da kuma addu'o'i masu tsarki, saboda haka tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana yi wa kansa ruƙya idan ya yi rashin lafiya, haka nan yana yi wa wanda ya yi rashin lafiya daga iyalansa da wasunsu ruƙiyya.
- Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa yi wa mara lafiya addu'ar waraka tare da abinda ke cikin rashin lafiya na kankare zunubai da lada kamar yadda hadisai suka zo da hakan ya rikitar, to amsa ita ce: Lallai addu'a ibada ce, kuma bata kore lada da kuma kaffara; domin cewa su suna samuwane a farkon rashin lafiyar da kuma haƙuri a kanta, mai addu'a yana tsakanin kyawawa biyu: Kodai abin nufinsa ya samu, ko kuma a canja masa da jawo wani anfanin ko tunkuɗe cuta, kowanne daga cikinsu daga falalar Allah ne.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 134) (5750).
صحيح مسلم (4/ 1721) (2191).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 162).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 477).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (11/ 539).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 687).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضيَ اللهُ عنه: أَنَّ جِبْرِيلَ أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ اشْتَكَيْتَ؟ فَقَالَ: «نَعَمْ» قَالَ: «بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ، مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ، مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ، اللهُ يَشْفِيكَ بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ».
Daga Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi -: Cewa (Mala’ika) Jibril ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Muhammad baka da lafiya ne? sai ya ce: «Eh» ya ce: «Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya tambaye shi: Ya Muhammad kana fama da rashin lafiya ne? Sai ya ce: Eh. Sai Mala’ika Jibril ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa ruƙya da faɗinsa: «Da sunan Allah» ina mai neman taimakonSa «Nake maka ruƙya» nake nema maka tsari. «Daga dukkan abinda yake cutar da kai» ƙarami ne ko babba. «Daga kowace rai» mummuna. «Ko maitar mai hassada» da ya kai gareka, Allah «Ya warkar da kai» kuma ya kareka daga dukkanin cutuka. «Da sunan Allah nake maka ruƙya» ya maimaita shi ne dan kai matuƙa, kuma ya fara da shi kuma ya rufe da shi dan nuni zuwa ga cewa babu wani mai amfanarwa sai Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.
Fa’idoji
- Halaccin labarta rashin lafiya dan bayanin waƙi'in hali ba dan babin rashin haƙuri da kai kuka ba.
- Ruƙya tana halatta da sharuɗɗan nan masu zuwa: 1- Ta zama da Alƙur'ani ne ko da ambatan sunan Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma addu'o'in da aka shara'anta. 2- Ta zama da harshen larabci, ko da abinda ake sanin ma'anarsa daga wasu harsunan daban. 3- Ya ƙudirce cewa ruƙya ita akan kanta bata tasiri; kawai ita sababi ce daga cikin sabubban da basa tasiri sai da izinin Allah - Mai girma da ɗaukaka -. 4- Ta kaɗaita daga shirka, ko abinda aka haramta, ko bidi'a, ko abinda zai kai zuwa ga hakan.
- Tabbatar da cutar lambing baka ( ko maita), kuma cewa ita gaskiya ce, to yana kamata a nemi yin ruƙya daga gareta.
- An so yin ruƙya da abinda ya zo a cikin hadisi.
- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar waninsa ne daga mutane, duk abinda yake samun waninsa na rashin lafiya zai iya samunsa.
- Kulawar Allah ga AnnabinSa- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kiyayeShi, da wakilta mala'ikunSa da hakan.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 1718) (2186).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 164).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص538).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 485).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (11/ 568).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 690).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عُثْمَانَ بْنِ أَبِي الْعَاصِ الثَّقَفِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ شَكَا إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَجَعًا يَجِدُهُ فِي جَسَدِهِ مُنْذُ أَسْلَمَ، فَقَالَ لَهُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «ضَعْ يَدَكَ عَلَى الَّذِي تَأَلَّمَ مِنْ جَسَدِكَ، وَقُلْ بِاسْمِ اللهِ ثَلَاثًا، وَقُلْ سَبْعَ مَرَّاتٍ أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ».
Daga Usman ɗan Abul Aas al-Saƙafi - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya kai kukan wani ciwo da yake jinsa a cikin jikinsa wajen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tunda ya musulunta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wani ciwo ya kama Uman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya kusa ya halakar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo l ya duba shi, kuma ya sanar da shi wata addu'ar da Allah zai ɗauke masa abinda ya saukar masa na rashin lafiyar; shi ne ya ɗora hannunsa akan wurin da yake jin ciwon, kuma sai ya ce: Bismillah, (Da sunan Allah) sau uku, sannan ya ce sau bakwai: (Ina neman tsari) ina fakewa kuma ina katanguwa (Da Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji)na raɗaɗi a wannan lokacin (kuma nake tsoro) nake jin tsoron faruwarsa a nan gaba na baƙin ciki da tsoro, ko ya wannan cutar ta ci gaba kuma radadinta ya yadu a jiki.
Fa’idoji
- An so mutum ya yi wa kansa tawaida kamar ydda ya zo a cikin hadisin.
- Kai kuka - ba tare da kurari ba ko bijirewa - ba ya kore dogaro (ga Allah) da kuma haƙuri.
- Addu'a tana daga jumlar aikata sabubba, saboda haka yana kamata a takaitu da lafazzukanta da kuma adadinta.
- Wannan addu'ar tana kasancewa ne ga dukkan wani raɗaɗi na gaɓa.
- Ɗora hannu akan wurin raɗaɗi a lokacin yin tawaida da wannan addu'ar.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 1728) (2202).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 163).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 481).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، لعبدالرؤوف المناوي (1/ 284).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 689).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يَتَعَوَّذُ مِنَ الجَانِّ، وعَيْنِ الإنسان، حتى نَزَلَتْ المُعَوِّذتان، فلمَّا نَزَلَتا، أخذ بهما وتركَ ما سواهما.
An rawaito daga Abu Sa'id Al-khudri -Allah ya yarda da shi- ya ce:Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi-ya Kasance yana neman tsari daga Aljani da kuma Kanbun baka" har Falaki da Nasi suka sauka, yayin da suka sauka, sai ya dauke su yabar wasunsu"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
1-بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف: سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي ، سنة النشر: 1418 هـ- 1997م
2-الجامع الصحيح –وهو سنن الترمذي-؛ للإمام محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق الشيخ أحمد شاكر، مكتبة الحلبي-مصر، الطبعة الثانية، 1388هـ.
3-رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ.
4-سنن ابن ماجه؛ للحافظ محمد بن يزيد القزويني، حققه محمد فؤاد عبدالباقي، دار إحياء الكتب العربية.
5-السنن الصغرى للنسائي "المجتبى"، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، نشر: مكتب المطبوعات الإسلامية – حلب، الطبعة: الثانية، 1406ه – 1986م.
6-كنوز رياض الصالحين؛ فريق علمي برئاسة أ.د. حمد العمار، دار كنوز إشبيليا-الرياض، الطبعة الأولى، 1430هـ.
7-مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.
8-مشكاة المصابيح؛ تأليف محمد بن عبدالله التبريزي، تحقيق محمد ناصر الدين الألباني، المكتب الإسلامي-بيروت، الطبعة الثانية، 1399هـ.
9-نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
10- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين, محمد علي بن محمد البكري الصديقي الشافعي, اعتنى بها: خليل مأمون شيحا, الناشر: دار المعرفة للطباعة والنشر والتوزيع، بيروت – لبنان, الطبعة: الرابعة، 1425 هـ - 2004 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ عَادَ مَرِيضًا، لَمْ يَحْضُرْ أَجَلُهُ فَقَالَ عِنْدَهُ سَبْعَ مِرَارٍ: أَسْأَلُ اللَّهَ الْعَظِيمَ رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيَكَ، إِلَّا عَافَاهُ اللَّهُ مِنْ ذَلِكَ الْمَرَضِ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani musulmin da zai ziyarci wani musulmi a cikin rashin lafiyarsa wanda lokacin mutuwarsa bai yi ba, sannan mai ziyarar ya yi wa mara lafiya addu'a da faɗinsa: (Ina roƙon Allah Mai girma) a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, (Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya), kuma ya maimaitata hakan sau bakwai sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar.
Fa’idoji
- An so addu'a ga mara lafiya da wannan addu'ar, da kuma maimaitata sau bakwai.
- Tabbatar da waraka ga wanda aka faɗi wannan addu'ar a wurinsa da izinin Allah - Maɗaukakin sarki -, in ta bijiro da gaskiya da kuma salaha.
- Zai faɗi wannan addu'ar ne a ɓoye da bayyane, dukkan hakan ya halatta, sai dai idan ya jiyar da mara lafiyar to shi ya fi; domin a cikinsa akwai shigar da farin ciki gare shi.
Madogara
سنن أبي داود (5/ 22) (3106).
سنن الترمذي (3/ 593) (2083).
السنن الكبرى للنسائي (9/ 385) (10820).
مسند أحمد (4/ 40) (2137).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 163).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص537).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 483).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (11/ 559).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 689).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com