Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «انْصُرْ أَخَاكَ ظَالِمًا أَوْ مَظْلُومًا». فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَنْصُرُهُ إِذَا كَانَ مَظْلُومًا، أَفَرَأَيْتَ إِذَا كَانَ ظَالِمًا كَيْفَ أَنْصُرُهُ؟ قَالَ: « تَحْجُزُهُ -أَوْ تَمْنَعُهُ- مِنَ الظُّلْمِ؛ فَإِنَّ ذَلِكَ نَصْرُهُ».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta». Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? ya ce: «Ka kare shi - ko ka hana shi - daga zalinci; domin cewa hakan taimakonsa ne».
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi da ya taimaki ɗan'uwansa musulmi, daidai ne ya kasance azzalimi ne ko wanda aka zalinta, sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shi ne in hana a zalince shi, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? Ya ce: Ka hana shi ka yi riƙo da hannunsa ka kare shi, ka hana shi zalincin; domin hakan shi ne taimakonsa akan Shaiɗaninsa da kuma ransa mai umartarsa da mummunan aiki.

Fa’idoji
  1. Faɗakarwa akan wani haƙƙi daga cikin haƙƙoƙin 'yan uwantaka ta imani tsakanin musulmai.
  2. Riƙo da hannun azzalimi, da kuma hana shi zalinci.
  3. Yadda Musulunci ya saɓawa fahimce-fahimcen Jahiliyya, inda suka kasance suna taimakekeniya, duk ɗayane sun kasance waɗanda aka zalinta ne ko masu zalintar wasunsu ne.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 128) (2443). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 589). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 326).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZAMANTAKEWAR MUSULMI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com