Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ZAMANTAKEWAR MUSULMI

Hadisai 6

Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لَيْسَ الْوَاصِلُ بِالْمُكَافِئِ، وَلَكِنِ الْوَاصِلُ الَّذِي إِذَا قُطِعَتْ رَحِمُهُ وَصَلَهَا».
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari, Cewa cikakken mutum a sada zumunci da kuma kyautatawa 'yan uwa shi ne mutumin da yake fuskantar kyakkyawa da kyakkywa, Kai mai sadarwa a hakika a sada zumunci shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi, idan sun munana masa to sai shi ya fuskantarsu da kyautatawa zuwa garesu.

Fa’idoji
  1. Sada zumunci abin la'akari a shari'a shi ne ka sadarwa wanda ya yanke maka daga gare su, ka yi afuwa ga wanda ya zalinceka, ka bawa wanda ya haramta maka, bawai sadarwar fuskanta da sakayya ba.
  2. Sada zumunci yana kasancewane ta hanyar sadar da abinda zai yiwu na alheri na dukiya da addu'a, da horo da aikin alheri, da kuma hani daga abin ki da makamantansu, da kuma tunkude abinda zai yiwu na sharri daga gare su.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 6) (5991). منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة محمد قاسم (5/ 242). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 397). نزهة المتقين، لمصطفى الخن وغيره (1/ 311). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 190).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «انْصُرْ أَخَاكَ ظَالِمًا أَوْ مَظْلُومًا». فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَنْصُرُهُ إِذَا كَانَ مَظْلُومًا، أَفَرَأَيْتَ إِذَا كَانَ ظَالِمًا كَيْفَ أَنْصُرُهُ؟ قَالَ: « تَحْجُزُهُ -أَوْ تَمْنَعُهُ- مِنَ الظُّلْمِ؛ فَإِنَّ ذَلِكَ نَصْرُهُ».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta». Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? ya ce: «Ka kare shi - ko ka hana shi - daga zalinci; domin cewa hakan taimakonsa ne».
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi da ya taimaki ɗan'uwansa musulmi, daidai ne ya kasance azzalimi ne ko wanda aka zalinta, sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shi ne in hana a zalince shi, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? Ya ce: Ka hana shi ka yi riƙo da hannunsa ka kare shi, ka hana shi zalincin; domin hakan shi ne taimakonsa akan Shaiɗaninsa da kuma ransa mai umartarsa da mummunan aiki.

Fa’idoji
  1. Faɗakarwa akan wani haƙƙi daga cikin haƙƙoƙin 'yan uwantaka ta imani tsakanin musulmai.
  2. Riƙo da hannun azzalimi, da kuma hana shi zalinci.
  3. Yadda Musulunci ya saɓawa fahimce-fahimcen Jahiliyya, inda suka kasance suna taimakekeniya, duk ɗayane sun kasance waɗanda aka zalinta ne ko masu zalintar wasunsu ne.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 128) (2443). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 589). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 326).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Zai fi kyau mai bi wanda yake cudanya da mutane kuma yake haƙuri da ciwon su fiye da wanda ba ya cudanya da mutane kuma ya haƙura da musibar su.

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «المؤمن الذي يخالط الناس، ويصبر على أذاهم خير من الذي لا يخالط الناس ولا يصبر على أذاهم».
Daga Abdullahi bn Omar - Allah ya yarda da shi - a kan annabi - salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Mumini wanda yake cudanya da mutane kuma ya yi hakuri da cutarwarsu ya fi wanda ba ya cakuduwa da mutane kuma ya yi hakuri da cutarwarsu".
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wannan hadisi hujja ce a kan falalar cuxanya da mutane da ganawa da su, kuma mumini wanda ya shiga cikin mutane ya sadu da su, kuma ya yi haquri da cutarwar da za ta same shi saboda nasiharsu da shiriyar su, ya fi mumini wanda ba ya cudanya da mutane, amma ya kasance banda taruwarsu kuma yana janyewa daga gare su ko yana zaune shi kaxai, saboda ba ya haquri da shi Cutar da su.

Madogara

سنن الترمذي، لمحمد بن عيسى بن سَوْرة الترمذي، أبو عيسى، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر (جـ 1، 2)، ومحمد فؤاد عبد الباقي (جـ 3)، وإبراهيم عطوة عوض (جـ 4، 5)، ط شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر. سنن ابن ماجه، لابن ماجة أبو عبد الله محمد بن يزيد القزويني، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، ط دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي. صحيح الجامع الصغير وزيادته، لأبي عبد الرحمن محمد ناصر الدين الألباني، ط المكتب الإسلامي. توضيح الأحكام من بلوغ المرام، الشيخ عبد الله بن عبد الرحمن البسام، ط مكتبة الأسد الإسلامية، الطبعة الخامسة. منحة العلام في شرح بلوغ المرام، الشيخ عبد الله بن صالح الفوزان، ط دار ابن الجوزي، الطبعة الأولى. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، الشيخ صالح الفوزان بن عبد الله الفوزان، طبعة الرسالة فتح ذي الجلال والإكرام، الشيخ محمد بن صالح العثيمين، ط المكتبة الإسلامية، الطبعة الأولى. سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للإمام محمد بن إسماعيل الصنعاني، ط دار الحديث.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina"

عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : "إنَّ الأشعريين إذا أرمَلُوا في الغَزْوِ، أو قَلَّ طعامُ عِيالِهم بالمدينةِ، جَمَعُوا ما كان عندهم في ثوبٍ واحدٍ، ثم اقتَسَمُوه بينهم في إناءٍ واحدٍ بالسَّوِيَّةِ، فَهُم مِنِّي وأنا مِنهُم".
An rawaito daga Abu Musa Al-Ash'ari -Allah ya yarda da shi- ya ce Annabi SAW ya ce: "Lallai Kabilar Ash'ariyawa idan Mujinsu ya Mutu a wajen yaki, ko Abincin Iyalansu ya ragu a Madina sai su hada abunda yake wurin su a cikin Zani daya, sannan sai su raba shi tsakaninsu acikin kwarya daya, daidai da dai dai, Saboda haka ni daga cikin su nake suma kuma nawa ne"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lallai Ash'ariyawa, wadanda su ne mutanen Abu Musa, yardar Allah ta tabbata a gare shi, idan abincinsu ya ragu ko kuma suna cikin mamayar jihadi saboda Allah, sai su tattara abincinsu su raba daidai a tsakaninsu, don haka sun cancanci ba wa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wani kaso na girmamawa da soyayya, kuma shi ma yana cikinsu, amincin Allah ya tabbata a gare shi, gwargwadon hanyar su a wannan. kuma wajibine na biyayya.

Madogara

صحيح البخاري , ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار طوق النجاة, الطبعة: الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم, ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار إحياء التراث العربي, بيروت. فتح الباري لابن حجر العسقلاني ,رقم كتبه وأبوابه وأحاديثه: محمد فؤاد عبد الباقي- قام بإخراجه وصححه وأشرف على طبعه: محب الدين الخطيب- عليه تعليقات العلامة: عبد العزيز بن عبد الله بن باز.دار المعرفة, ط بدون, 1379ه. شرح مسلم للنووي, دار إحياء التراث, ط2, 1392ه. تطريز رياض الصالحين لفيصل بن عبد العزيز المبارك النجدي, تحقيق: عبد العزيز آل حمد, دار العاصمة , الطبعة: الأولى، 1423هـ. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي, دار ابن الجوزي،الطبعة الأولى 1418ه. شرح رياض الصالحين لابن عثيمين , دار الوطن للنشر، الرياض, الطبعة: 1426 هـ. كنوز رياض الصالحين بإشراف حمد العمار, دار كنوز إشبيليا, الطبعة الأولى, 1430ه. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين, مؤسسة الرسالة, الطبعة الرابعة عشرة, 1407ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

‌Lallai Allah Ya yardar muku da abubuwa uku, kuma Yana ƙin abubuwa uku a gareku

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللهَ يَرْضَى لَكُمْ ثَلَاثًا، وَيَكْرَهُ لَكُمْ ثَلَاثًا، فَيَرْضَى لَكُمْ: أَنْ تَعْبُدُوهُ، وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَأَنْ تَعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا، وَيَكْرَهُ لَكُمْ: قِيلَ وَقَالَ، وَكَثْرَةَ السُّؤَالِ، وَإِضَاعَةِ الْمَالِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Allah Ya yardar muku da abubuwa uku, kuma Yana ƙin abubuwa uku a gareku, Yana yardar muku: Ku bauta maSa, kada ku haɗa shi da wani abu a bauta, kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gabaɗaya kada ku rarraba. Kuma yana ƙi muku: Ƙila wa ƙala, da yawan roƙo, da kuma tozartar da dukiya».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Yana son ɗabi'u uku daga bayinSa, kuma Yana ƙin abubuwa uku daga gare su, Yana so daga garesu: Su kaɗaita Shi da bauta kada su taranya wani abu a cikin bautarSa, kuma su yi riƙo da alƙawarin Allah da kuma Alƙur'ani da sunnar AnnabinSa bakiɗaya, kada su rarraba daga jama'ar musulmai. Kuma yana ƙi musu: zance mara anfani da yasasshiyar magana a cikin abinda babu ruwansu, da kuma tambayar abinda bai afku ba, ko roƙon mutane dukiyoyinsu, da kuma abinda ke hannunsu, da kuma abinda ba'a buƙatarsa, da tozarta dukiya da bada ita ba ta fuskar shari'a ba, da kuma bijiro da ita ga abinda zai lalata ta.

Fa’idoji
  1. Allah Yana son ikhlasi daga bayinSa a cikin bautarSa, kuma yana ƙin kafirci daga bayinsa.
  2. Kwaɗaitarwa akan riƙo da igiyar Allah - Maɗaukakin sarki -; saboda abinda ke cikinsa ha haɗuwar kai.
  3. Kwaɗaitarwa akan jama'a, da kuma umarni da lazimtarta da hada kai, da kuma hani daga kishiyarta na rarrabuwa da kuma saɓani.
  4. Hani daga yawan zancen da ba shi da amfani; domin idan ya kasance abin halattawa ne to a cikinsa akwai bata lokaci, idan kuma haramun ne to a cikinsa akwai yawan zunubi.
  5. Barin kutsawa a cikin labarun mutane da kuma bibiyar halayensu da kwaikwayar maganganunsu da kuma ayyukansu.
  6. Hani daga yawan roƙon dukiyoyin mutane.
  7. Haramta lalatar da dukiya, da kuma kwaɗaitarwa akan kiyayeta a abinda yake anfanarwa.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1340) (1715). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (30/ 85). إكمال المعلم بفوائد مسلم (5/ 568).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?

عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِأَفْضَلَ مِنْ دَرَجَةِ الصِّيَامِ وَالصَّلاَةِ وَالصَّدَقَةِ؟» قَالُوا: بَلَى، قَالَ: «صَلاَحُ ذَاتِ البَيْنِ، فَإِنَّ فَسَادَ ذَاتِ البَيْنِ هِيَ الحَالِقَةُ».
Daga Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?" Suka ce: Eh, ya ce: "Yin sulhu tsakanin waɗanda ke rigima, domin ɓacin tsakanin waɗanda ke rigima shine mai askewa".
Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin bana baku labarin abin da ya fi ladan nafilar azimi da sallah da sadaka ba? Suka ce: Eh.. Ya ce: Yin sulhu tsakaknin masu rigima inda rigima take gadar da rabuwa da kuma kadaita da ƙiyayya da juyawa juna baya tsakanin mutane, domin abin da yake haifuwa akan ɓata waɗanda ke rigima na ƙiyayya wacce ita ce ɗabi'ar da sha'aninta shine ta halakar ta tunɓuke Addini da duniya kamar yadda aska take tunɓuke gashi.

Fa’idoji
  1. Shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta hanyar tambayar sahabbai da kuma sasu shauƙin sanin amsa.
  2. Ɗaibi ya ce: Kwaɗaitarwa a kan sulhunta masu rigima da nisantar ɓata su; domin yin sulhu sababi ne na yin riƙo da igiyar Allah da kuma rashin rabuwa tsakanin musulmai, ɓacin masu rigima rabuwa ne a cikin Addini duk wanda ya yi sulhu ya kuma ɗauke ɓacinta zai samu daraja sama da abin da mai azimi mai tsayuwar dare mai shagalta da keɓantuwar kansa yake samu.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 280) (4919). سنن الترمذي (4/ 244) (2509). تحفة الأحوذي (7/ 179). شرح سنن أبي داود للعباد (559/ 32).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com