Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا أَسْفَلَ مِنَ الكَعْبَيْنِ مِنَ الإِزَارِ فَفِي النَّارِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi maza daga sakin dukkan abinda yake suturce jikinsu tufa ne ko wanduna ko waninsu ƙasa da idan sawun diga-digai, kuma abinda ke ƙasan idan sawu na ƙafar mai mayafin da ya sake shi to shi yana cikin wuta dan yi masa uƙuba akan aikinsa.

Fa’idoji
  1. Hani daga tsawaita tufa zuwa abinda ke ƙasa da idan sawu ga maza, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
  2. Ibnu Hajar ya ce: An togance abinda ya sake shi ƙasa dan lalurara daga sakin mayafi; misali kamar wanda idan sawunsa akwai ciwon da yake cutar da shi idan bai rufe shi da mayafin ba inda bai samu waninsa ba.
  3. Wannan hukuncin ya keɓanci maza ne; domin cewa mata an umarcesu da su saki mayafansu ƙasa da idan sawu har zuwa tsawon zira'i.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 141) (5787). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (8/ 418). ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (23/ 76).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
TUFAFI DA KWALLIYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com