عن أبي موسى رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لا نِكَاحَ إِلّا بِوَليٍّ».
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu aure sai da waliyyi".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mace auranta ba ya inganta sai da waliyyin da zai tsaya a ɗaurin auren.
Fa’idoji
Waliyyi sharaɗi ne a ingancin aure, idan aure ya faru ba tare da waliyyi ba, ko mace ta aurar da kanta, to, aurenta bai inagnta ba.
Waliyyi shi ne mafi kusancin mazaje ga mace, wani waliyyi na nesa ba zai aurar da ita ba, tare da samuwar waliyyi na kusa.
An sharɗanta (wasu) sharuɗɗa ga waliyyi: Ya zama mukallafi, kuma namiji, da shiriya a sanin maslahohin aure, da haɗuwar Addini tsakanin waliyyi da wanda zai yi wa walicci, duk wanda bai siffantu da waɗannan siffofin ba, to bai cancanci zama waliyyi a ɗaura aure ba.
Madogara
سنن أبي داود (3/ 427) (2085).
سنن الترمذي (2/ 392) (1101).
سنن ابن ماجه (3/ 79) (1881).
مسند أحمد (32/ 280) (19518).
البدرُ التمام شرح بلوغ المرام، للمَغرِبي (7/ 57).
إرواء الغليل في تخريج أحاديث منار السبيل، للألباني (6/ 237).
توضِيح الأحكام من بلوغ المَرَام، للبسام (5/ 262).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (7/ 222).
فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (4/ 469).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com