Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku yi wa juna kyauta, za ku so juna

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «تَهَادَوا تَحَابُّوا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku yi wa juna kyauta, za ku so juna».
Buhari a cikin Al-Adab Al-Mufrad da Abu Ya'la da Baihakisuka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan cewa Musulmi tare da ɗan'uwansa su dinga yawan kyaututtuka, kuma kyauta tana daga cikin sabubban soyayya da haɗuwar zuciya.

Fa’idoji
  1. An so yin kyauta; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ita.
  2. Kyuata sababi ce ta (samun) soyayya.
  3. Yana kamata ga mutum ya aikata dukkanin abin da zai jawo soyayya tsakakaninsa da mutane, daidai ne a kyauta ne ko a tausasa lamura ne, ko a magana mai kyau, ko a sakin fuska gwargwadan ikonsa.
Madogara

الأدب المفرد للبخاري (ص:208) (594). مسند أبي يعلى الموصلي (11/ 9) (6148). السنن الكبرى للبيهقي (6/ 169). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام (4/ 319). فيض القدير (3/ 271). التيسير بشرح الجامع الصغير (1/ 457).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KYAUTA DA KYAUTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com