عن عائشة رضي الله عنها قالت: يا رسولَ اللهِ، إِنَّ لِي جَارَيْنِ، فإلى أَيِّهِمَا أُهْدِي؟ قال: «إلى أَقْرَبِهِمَا مِنْكِ بَابًا».
A hadisin A’isha yardar Allah ta tabbata a gare ta wacce ta ce: Ya Manzon Allah, ina da makwabta biyu, to a ba ni wa? Ya ce: «Zuwa ga mafi kusantar su da kai».
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A’isha yardar Allah ta tabbata a gare ta, ta tambayi Annabi mai tsira da amincin Allah :: Ina da makwabta biyu, kuma an umarce ni da girmama makwabci kwata-kwata. Ba zan iya keɓe su ga duka biyun ba, to wanne ne daga cikinsu aka ba ni domin in shiga cikin rukunin waɗanda ke girmama maƙwabcin? Shi, Allah ya kara yarda a gare shi, ya ce: "Ga mafi kusancinku kofa ce."
Madogara
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الرابعة عشر، 1407ه - 1987م.
رياض الصالحين للنووي، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، ط1، 1428هـ.
رياض الصالحين، للنووي، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، ط4، 1428هـ.
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن سهل بن سعد رضي الله عنه : أن امرأةَ جاءت إلى رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم بِبُرْدَةٍ مَنسُوجَةٍ، فقالت: نَسَجتُها بيديَّ لأَكْسُوَكَها، فأخذها النبيُّ صلى الله عليه وسلم محتاجاً إليها، فخرجَ إلينا وإنها إزارُهُ، فقال فلانٌ: اكسُنِيها ما أحسَنَها! فقال: "نعم"، فجلسَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم في المجلسِ، ثم رجع فطَوَاها، ثم أرسلَ بها إليه، فقال له القومُ: ما أحسَنتَ! لبسها النبيُّ صلى الله عليه وسلم محتاجاً إليها، ثم سألته وعَلِمتَ أنه لا يَرُدَ سائلاً، فقال: إني واللهِ ما سألتُهُ لألبِسَها، إنما سألتُهُ لتكُونَ كَفَنِي. قال سهلٌ: فكانت كَفَنَهُ.
A kan Sahl bin Saad - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa wata mata ta zo wajan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da alkyabba mai suttura.ta ce nayi ta ne da hannuna sai Manzon ya karveta yana mai bukatarta sai ya futo mana wani lokaci ya daure da ita sai wani Mutum ya ce ka bani ita banga abu mafi kyawunta! ba Ya ce: "To." Don haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zauna a cikin majalisin, sannan ya dawo ya ninke ta sannan ya aika masa da ita, sai mutanen suka ce masa: baka kyauta ba Annabi - SAW- ya sanya ta cikin buqata, sai ka tambaye shi kuma kasan cewa bai hana wanda ya tambaye shi, sai ya ce: Wallahi ban nemi ya bani badon insanya, amma ni natambaye shi ne don ta zama likkafanina na. Sahl ya ce: ita ce Likafaninsa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Kwatankwacin saDarajaIngantacce ne
Madogara
بهجة شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي.
تطريز رياض الصالحين؛ تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبدالعزيز آل حمد، دار العاصمة-الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.
تيسير العزيز الحميد في شرح كتاب التوحيد؛ للإمام سليمان بن عبدالله بن محمد بن عبدالوهاب، تحقيق أسامة عطايا، دار الصميعي-الرياض، الطبعة الأولى، 1428هـ.
الجمع بين الصحيحين؛ للإمام محمد بن فتوح الحميدي، تحقيق د. علي البواب، دار ابن حزم.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، دار الكتاب العربي-بيروت.
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ.
صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبدالله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
فتح الباري بشرح صحيح البخاري؛ للحافظ أحمد بن علي بن حجر العسقلاني، دار المعرفة-بيروت.
كنوز رياض الصالحين؛ فريق علمي برئاسة أ.د. حمد العمار، دار كنوز إشبيليا-الرياض، الطبعة الأولى، 1430هـ.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن الصعب بن جَثَّامَةَ رضي الله عنه ، قال: أهديتُ رسولَ الله - صلى الله عليه وسلم - حماراً وحشياً، فَرَدَّهُ عَلَيَّ، فلما رأى ما في وجهي، قال: «إنا لم نَرُدَّهُ عليك إلا لأنَّا حُرُمٌ».
An rawaito daga Al-Sa'ab Bn Jathama -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Na yi Kyautar Jakin dawa ga Manzon Allah -tsra da Amincin Allah su abbata a gare shi Sai ya dawo da shi waje na, yayin da yaga abunda ke fuskata, ya ce: Mu ba mu dawo ma da shi ba sai don muna cikin Harami "
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Daga cikin kyawawan halayensa - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne cewa bai yiwa mutane fadanci a cikin addinin Allah ba, kuma bai rasa son faranta zukatansu ba - Al-Saab bin Jathamah - Allah ya yarda da shi - Annabi - SAW- ya wuce yana cikin Harami .Al-Saab bin Jothama ya kasance maharbin kiyayya, kuma lokacin da Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya wuce shi, sai ya kama jakin daji, sai Annabi - SAW- ya mayar masa da shi.Sannan sai fuskarsa ta canza, kuma lokacin da ya ga abin da ke fuskarsa, kyakkyawar zuciya, kuma ya gaya masa cewa bai mayar masa da ita ba face saboda yana cikin Harami ne, kuma Mai Harami baya cin abinci da aka farau to..
Madogara
بهجة شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي.
تطريز رياض الصالحين؛ تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبدالعزيز آل حمد، دار العاصمة-الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ.
شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن-الرياض، 1426هـ.
صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبدالله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبدالباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
فتح الباري بشرح صحيح البخاري؛ للحافظ أحمد بن علي بن حجر العسقلاني، دار المعرفة-بيروت.
كنوز رياض الصالحين؛ فريق علمي برئاسة أ.د. حمد العمار، دار كنوز إشبيليا-الرياض، الطبعة الأولى، 1430هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي حُمَيْدٍ السَّاعِدِيِّ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: اسْتَعْمَلَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا عَلَى صَدَقَاتِ بَنِي سُلَيْمٍ، يُدْعَى ابْنَ اللُّتْبِيَّةِ، فَلَمَّا جَاءَ حَاسَبَهُ، قَالَ: هَذَا مَالُكُمْ وَهَذَا هَدِيَّةٌ. فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَهَلَّا جَلَسْتَ فِي بَيْتِ أَبِيكَ وَأُمِّكَ، حَتَّى تَأْتِيَكَ هَدِيَّتُكَ إِنْ كُنْتَ صَادِقًا» ثُمَّ خَطَبَنَا، فَحَمِدَ اللَّهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ، ثُمَّ قَالَ: «أَمَّا بَعْدُ، فَإِنِّي أَسْتَعْمِلُ الرَّجُلَ مِنْكُمْ عَلَى العَمَلِ مِمَّا وَلَّانِي اللَّهُ، فَيَأْتِي فَيَقُولُ: هَذَا مَالُكُمْ وَهَذَا هَدِيَّةٌ أُهْدِيَتْ لِي، أَفَلاَ جَلَسَ فِي بَيْتِ أَبِيهِ وَأُمِّهِ حَتَّى تَأْتِيَهُ هَدِيَّتُهُ، وَاللَّهِ لاَ يَأْخُذُ أَحَدٌ مِنْكُمْ شَيْئًا بِغَيْرِ حَقِّهِ إِلَّا لَقِيَ اللَّهَ يَحْمِلُهُ يَوْمَ القِيَامَةِ، فَلَأَعْرِفَنَّ أَحَدًا مِنْكُمْ لَقِيَ اللَّهَ يَحْمِلُ بَعِيرًا لَهُ رُغَاءٌ، أَوْ بَقَرَةً لَهَا خُوَارٌ، أَوْ شَاةً تَيْعَرُ» ثُمَّ رَفَعَ يَدَهُ حَتَّى رُئِيَ بَيَاضُ إِبْطِهِ، يَقُولُ: «اللَّهُمَّ هَلْ بَلَّغْتُ» بَصْرَ عَيْنِي وَسَمْعَ أُذُنِي.
Daga Abu Humaid al-Sa'idi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne».
Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗorawa wani mutum aiki ana ce masa: Ibnul Lutbiyyah, shi ne aikin tattaro zakka daga ƙabilar Banu Sulaim, lokacin da ya dawo Madina sai ya yi masa bayani akan abinda ya karɓa da kuma abinda ya yi amfani da shi, sai Ibnul Lutbiyyah ya ce: Wannan dukiyarku ce wacce na tattarota ta zakka, wannan dukiyar kuma anbani kyautarta ne. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Shin ba zaka zauna acikin gidan babanka da babarka ba ka duba ka gani shin za’a baka kyautar idan kai mai gaskiya ne; domin cewa haƙƙoƙin da ka yi aiki saboda su sune sababin baka kyauta, kuma da a ce ka zauna a cikin gidanka da ba'a baka kyautar komai ba, dan haka ba ya kamata gareka ka halartata saboda kawai ta sameka ta hanyar kyauta. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya hau minbari yana mai yin huɗuba alhali shi yana mai fushi, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sannan ya ce: Bayan haka lallai ni ina ɗorawa ɗayanku aiki akan abinda Allah Ya sanya mini tasarrufi a cikinsa na zakka da kuma ganimomi, sai wanda ya yi aikin ya zo, ya ce: Wannan naku ne wannan kuma kyauta ce da aka bani! Shin ba ya zauna a cikin gidan babansa da babarsa ba har kyautarsa ta zo masa, wallahi wani ba zai ɗauki wani abu ba daga abinda aka ba shi, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar alƙiyama akan wuyansa, idan abinda ya ɗauka raƙumi ne yana kukan raƙuma, ko saniya ce da take irin kukan shanu, ko akuya ce da take irin kukan akuyoyi. Sannan ya ɗaga hannayensa sosai har waɗanda ke zaune suka ga farin hammatarsa, sannan ya ce: Ya Allah na isar musu da hukuncin Allah. Sannan Abu Humaid al-Sa'idi - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa: Wannan abinda idona ya gani ne kuma kunnena ya ji shi.
Fa’idoji
- Shugaba ya bayyanawa ma'aikatan dake tare da shi abin da ake nema daga garesu da kuma abinda aka hanasu a cikin ayyukansu.
- Narko ga wanda yake karbar dukiyoyin mutane akan zalinci.
- Babu wani azzalimi sai ya zo da abinda ya yi zalincin da shi a ranar alƙiyama.
- Wajibi akan ma'aikaci a cikin kowane aiki daga cikin ayyukan daula (ƙasa) ya bada abinda aka wakilta shi a kansa, ba ya halatta gare shi ya karɓi kyautukan abinda yake rataye da aikinsa, idan kuma ya karɓa to ya maida su baitul mali, ba ya halatta gare shi ya ɗaukarwa kansa su, kuma domin cewa su tsani ne na sharri da kuma ɓata amana.
- Ibnu Baɗɗal ya ce: Hadisin ya yi nuni akan cewa yi wa ma'aikaci kyauta yana kasancewa ne dan godewa aikin alherinsa ne, ko dan nuna soyayya gare shi, ko dan kwaɗayin abinda ya sanya shi na haƙƙi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi nuni zuwa cewa shi kamar ɗaya ne daga cikin musulmai a cikin abinda aka ba shi kyautar, ba shi da wani fifiko akansa a cikinsa, kuma shi ba ya halatta ya mallake shi.
- Nawawi ya ce: A cikin wannan hadisin akwai: Bayanin cewa kyautar ma'aikata haramun ce, kuma satar kayan ganima ne; domin cewa shi ya yi ha'inci a cikin shugabancinsa da kuma amanarsa, saboda haka ne a cikin hadisin aka ambaci uƙubarsa da kuma ɗaukar abinda aka ba shi kyautar a ranar alƙiyama, kamar yadda aka ambaci irinsa a kan wanda ya saci ganima, haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a cikin hadisin ya bayyana sababin haramta kyautar a kansa, kuma cewa ita da sababin shuganacin ce, saɓanin kyautar wanda ba ma'aikaci ba, ita mustahabbi ce.
- Ibnul Munir ya ce: Za'a fahimta daga faɗinsa; "Shin ba ya zauna a cikin gidan babansa da babarsa ba" halaccin karɓar kyauta daga wanda ya kasance yana ba shi kyauta kafin hakan. Ibnu Hajar ya ce: ba ya ɓoyuwa cewa bigiren hakan idan bai ƙaru akan al'ada ba.
- Usulubin Annabi a cikin nasiha shi ne gamewa ba wai yayatawa ba.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai halaccin yi wa wanda aka bawa amana hisabi.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai halaccin kwaɓar wanda ya yi kuskure.
- An so ɗaga hannaye a cikin addu'a.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 28) (6979).
صحيح مسلم (3/ 1463) (1832).
جمهرة اللغة، أبوبكر الأزدي (2/ 1067).
المعجم الوسيط، مجمع اللغة العربية (2/ 1065).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 305).
تطرز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص166).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 234).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: «حَمَلْتُ على فرس في سبيل الله، فأضاعه الذي كان عنده، فأردت أن أشتريه، وظننت أنه يبيعه بِرُخْصٍ، فسألت النبي صلى الله عليه وسلم ؟ فقال: لا تَشْتَرِهِ، ولا تعد في صدقتك؛ فإن أَعْطَاكَهُ بِدِرْهَمٍ؛ فإن العَائِدَ في هِبَتِهِ كالعَائِدِ في قَيْئِهِ».
Daga Umar -Allah ya yarda da shi- yace:"Na bayar da wani doki sabo da Allah,sai wanda dokin ke wajensa ya wulakantar da shi,sai naso in sayi dokin,don ina ganin zai sayar da shi da araha,sai na tambayi Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi-?sai yace: kar ka siya,kada ka karbe abin da kayi sadaka da shi,koda kuwa dirhami daya zai sayar maka da shi,don kuwa mai karbar kyautar da yayi,kamar mai yin amai ya lashe ne.".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya taimaki wani mutum akan jihadi a tafarkin Allah. sai ya bashi doki ya yi yaki a kansa, sai mutumin sai mutumin ya kasa ciyar da dokin, ba ya kula da shi, ya gajiyar da shu, har ya rame yayi rauni. Sai Umar yayi niyyar sayen dokin don ya san zai yi sauki sabo da ramewa da raunin da ya yi, sai dai bai yi cinikin dokin ba sai da ya shawarci Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- game da haka,sai Annabi ya hana shi sayen dokin komai araharsa, saboda wannan abu ne da aka bayar don Allah, kar ka damu da shi,sai ya zama kamar ka dawo da wani bangare na abin da ka bayar ne, don ka riga ka bayar, kuma an kankare zunubanka, datti ya fita daga gare ka, bai kamata ya komo gareka ba, wannan shi yasa aka ambaci cinikin da suna kome duk da cewa saye zai yi.
Madogara
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ.
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ.
عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم، لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ.
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما مرفوعاً: "العائد في هِبَتِهِ، كالعائد في قَيْئِهِ".
وفي لفظ: "فإن الذى يعود في صدقته: كالكلب يَقِئ ُثم يعود في قيئه".
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Mai fasa kyautarsa, kamar mai dawowa ne cikin Amansa" a cikin wani Lafazin kuma: "Domin wanda yake fasa sadakarsa: kamar Karenda yai amai kuma ya dawo yana lashe shi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi ya buga Misali ne don tsawatarwa daga fasa kyauta da mafi muni sura, ita ce ewa mai fasa kyautarsa, kamar kare ne wanda zai yi Amai sannan ya je ya lashe Amansa, sai ya ci daga abinda yake nuna Munin wannan halin nasa da kuma kaskascinsa, da kuma koma bayan wanda yayi hakan.
Madogara
- صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام-عبد الله البسام-تحقيق محمد صبحي حسن حلاق- مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426ه.
- منحة العلام في شرح بلوغ المرام:تأليف عبد الله الفوزان-طبعة دار ابن الجوزي-الطبعة الأولى 1428.
- فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام للشيخ ابن عثيمين- المكتبة الإسلامية القاهرة- تحقيق صبحي رمضان وأم إسراء بيومي- الطبعة الأولى 1427.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «تَهَادَوا تَحَابُّوا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku yi wa juna kyauta, za ku so juna».
Buhari a cikin Al-Adab Al-Mufrad da Abu Ya'la da Baihakisuka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan cewa Musulmi tare da ɗan'uwansa su dinga yawan kyaututtuka, kuma kyauta tana daga cikin sabubban soyayya da haɗuwar zuciya.
Fa’idoji
- An so yin kyauta; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ita.
- Kyuata sababi ce ta (samun) soyayya.
- Yana kamata ga mutum ya aikata dukkanin abin da zai jawo soyayya tsakakaninsa da mutane, daidai ne a kyauta ne ko a tausasa lamura ne, ko a magana mai kyau, ko a sakin fuska gwargwadan ikonsa.
Madogara
الأدب المفرد للبخاري (ص:208) (594).
مسند أبي يعلى الموصلي (11/ 9) (6148).
السنن الكبرى للبيهقي (6/ 169).
فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام (4/ 319).
فيض القدير (3/ 271).
التيسير بشرح الجامع الصغير (1/ 457).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com