Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu

عن ابنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم: «مَن تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu".
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane daga kafirai ko fasiƙai ko mutanen kirki - ta yadda zai aikata wani abu daga abin da ya keɓancesu daga aƙidu ko ibadu - to, yana daga cikinsu; domin kamanceceniya da su a zahiri yana kaiwa zuwa kamanceceniya da su a ɓoye, kuma babu kokwanto cewa kamanceceniya da mutane yana haifuwa ne daga sha'awarsu, kuma ya kan kai zuwa ga soyayyarsu da girmamasu da karkata zuwa garesu, wannan yana jan mutum zuwa ya yi kama da su har a ɓoye da ibada - Allah Ya yi mana tsari-.

Fa’idoji
  1. Gargaɗi daga kamanceceniya da kafirai da fasikai.
  2. Kwaɗaitarwa a kan kamanceceniya da mutanen kirki da koyi da su.
  3. Kamanceceniya a zahiri yana gadar da soyayya a ɓoye.
  4. Mutum yana samun narko da zunubi gwargwadon kamanceceniya da nau'inta.
  5. Hani daga kamanceceniya da kafirai a addininsu da al'adunsu waɗanda suka keɓanta da su, amma abin da bai zama irin hakan ba kamar neman sanin sana'o'i da makamancinsu, to, ba ya shiga a cikin hanin.
Madogara

سنن أبي داود (6/ 144) (4031). مسند أحمد (9/ 126) (5115). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 363). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 157). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 335). مشكاة المصابيح، للتبريزي (2/ 1246).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KWAIKWAYON DA AKA HANA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com