Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

KWAIKWAYON DA AKA HANA

Hadisai 4

Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَتَتَّبِعُنَّ سَنَنَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ، شِبْرًا بِشِبْرٍ، وَذِرَاعًا بِذِرَاعٍ، حَتَّى لَوْ دَخَلُوا فِي جُحْرِ ضَبٍّ لَاتَّبَعْتُمُوهُمْ» قُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ آلْيَهُودَ وَالنَّصَارَى؟ قَالَ: «فَمَنْ؟».
Daga Abu Sa'id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i, har da ko sun shiga ramin damo ne sai kun bi su" Muka ce: Ya manzon Allah ! Yahudawa da Nasara? ya ce: "To su wa?".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana bada labarin abinda halin da sashin al'ummarsa zasu kasance akansa bayan zamaninsa, shi ne bin hanyar Yahudawa da Nasara a aƙidunsu da ayyukansu da al'adunsu bi na zirfafawa mai tsanani taki da taki, zira'i da zira'i, har da a ce su shiga ramin damo to da waɗannan zasu shige shi suna bayansu.

Fa’idoji
  1. Alama daga alamomin annabtarsa inda ya bada labari da hakan kafin afkuwarsa sai ya afku kamar yadda ya bada labari.
  2. Hani daga kamanceceniyar musulmai da kafirai, daidai ne a cikin aƙidunsu ne ko ibadunsu ko bukukuwansu ko adonsu wanda ya keɓanta da su.
  3. Bayyana abubuwa na ma'ana da misalai da ake gani yana daga hanyoyin koyarwa a cikin muslunci.
  4. Damo; Wata dabba ce raminsa mai tsananin duhu ne mai wari, yana daga dabbobi masu jan ciki yana da yawa a sahara, kuma ta yadda aka keɓance ramin damo: Tsananin ƙuncinsa da muninsa, tare da hakan cewa su - saboda bin su ga sawunsu da bin hanyoyinsu - da ace (Yahudu da Nasara) zasu shiga misalin wannan ƙuncin mai muni da su ma sun bi su! Allah ne abin neman taimako.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 103) (7320). صحيح مسلم (4/ 2054) (2669). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص213). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص193).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu

عن ابنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم: «مَن تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu".
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane daga kafirai ko fasiƙai ko mutanen kirki - ta yadda zai aikata wani abu daga abin da ya keɓancesu daga aƙidu ko ibadu - to, yana daga cikinsu; domin kamanceceniya da su a zahiri yana kaiwa zuwa kamanceceniya da su a ɓoye, kuma babu kokwanto cewa kamanceceniya da mutane yana haifuwa ne daga sha'awarsu, kuma ya kan kai zuwa ga soyayyarsu da girmamasu da karkata zuwa garesu, wannan yana jan mutum zuwa ya yi kama da su har a ɓoye da ibada - Allah Ya yi mana tsari-.

Fa’idoji
  1. Gargaɗi daga kamanceceniya da kafirai da fasikai.
  2. Kwaɗaitarwa a kan kamanceceniya da mutanen kirki da koyi da su.
  3. Kamanceceniya a zahiri yana gadar da soyayya a ɓoye.
  4. Mutum yana samun narko da zunubi gwargwadon kamanceceniya da nau'inta.
  5. Hani daga kamanceceniya da kafirai a addininsu da al'adunsu waɗanda suka keɓanta da su, amma abin da bai zama irin hakan ba kamar neman sanin sana'o'i da makamancinsu, to, ba ya shiga a cikin hanin.
Madogara

سنن أبي داود (6/ 144) (4031). مسند أحمد (9/ 126) (5115). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 363). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 157). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 335). مشكاة المصابيح، للتبريزي (2/ 1246).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: لعن رسول الله صلى الله عليه وسلم الرجل يلبس لِبْسَةَ المرأة، والمرأة تلبس لِبْسَةَ الرجل.
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji.
Nasa'i ya rawaito shi cikin Alkubra da Ibnu Majah da ma'anarsa haka kuma Ahmad suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah ga dukkan namijin da ya yi kama da mace a cikin tufafin da suka keɓanci mata; daidai ne a cikin kama ne ko launi ko kaifiyya ko hanyar sanyawa da ado ko wanin haka. Ko mace ta yi kama da kayan da suka keɓanci maza kamar haka, kuma shi laifi ne babba daga manyan laifuka.

Fa’idoji
  1. AlShaukani ya ce: Haramcin kamanceceniyar mata da maza da maza da mata; domin cewa tsinuwa ba ta kasancewa sai akan aikata haram.
  2. Ibnu Usaimin ya ce: Abinda ya kasance abin tarayya ne tsakaninsu misalin sashin fanilolin da maza da mata suke sanyawa to cewa wannan babu laifi da shi, wato babu laifi maza da mata su ɗaura su; domin cewa shi sun yi tarayya ne.
Madogara

سنن أبي داود (6/ 195) (4098). السنن الكبرى للنسائي (8/ 297) (9209). سنن ابن ماجه (3/ 95) (1903). مسند أحمد (14/ 61) (8309). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1122). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (19/ 337). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 150). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 370).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai Yahudawa da Kiristoci basa rina gashinsu to ku sava Musu

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إن اليهود والنصارى لا يصبغون، فخالفوهم».
Daga Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Lallai Yahudawa da Kiristoci basa rina gashinsu to ku sava Musu"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 ه.ـ صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ. صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هــ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com