Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)
عن أبي هريرة رضي الله عنه أَن النبيَّ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم قَالَ: «الرَّجُلُ عَلَى دِينِ خَلِيلِهِ، فَلْيَنْظُر أَحَدُكُم مَنْ يُخَالِل».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum yana kamanceceniya da abokinsa amintacce a rayuwarsa da kuma al'adarsa, kuma abokantaka tana tasiri a ɗabi'u da yanayi da tasarrufi, saboda haka ne ya nunar zuwa kyakkyawan zabin aboki; domin aboki yana shiryar da abokinsa akan imani da shiriya da alheri, kuma yana kasancewa taimako ga abokinsa.
Fa’idoji
Umarni da abokantaka da zababbu da kuma tsabosu, da hani daga abokantaka da mutanen banza.
An kebanci aboki banda ɗan'uwa; domin aboki kai ne wanda ka zabe shi, amma ɗan'uwa da makusanci to kai baka da zabi a cikinsa.
Zabin aboki babu makawa dole sai an yi tunani.
Mutum yana karfafar addininsa ta hanyar abokantakar muminai, kuma yana raunana shi ta hanyar abokantaka da fasikai.
Madogara
سنن أبي داود (7/ 204) (4833).
سنن الترمذي (4/ 187) (2378).
مسند أحمد (13/ 398) (8028).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 433).
تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، للمباركفوري (7/ 51).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص250).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 166).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 341).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com