Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCE-HUKUNCEN ƘAUNA DA BARRANTA

Hadisai 3

Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)

عن أبي هريرة رضي الله عنه أَن النبيَّ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم قَالَ: «الرَّجُلُ عَلَى دِينِ خَلِيلِهِ، فَلْيَنْظُر أَحَدُكُم مَنْ يُخَالِل».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum yana kamanceceniya da abokinsa amintacce a rayuwarsa da kuma al'adarsa, kuma abokantaka tana tasiri a ɗabi'u da yanayi da tasarrufi, saboda haka ne ya nunar zuwa kyakkyawan zabin aboki; domin aboki yana shiryar da abokinsa akan imani da shiriya da alheri, kuma yana kasancewa taimako ga abokinsa.

Fa’idoji
  1. Umarni da abokantaka da zababbu da kuma tsabosu, da hani daga abokantaka da mutanen banza.
  2. An kebanci aboki banda ɗan'uwa; domin aboki kai ne wanda ka zabe shi, amma ɗan'uwa da makusanci to kai baka da zabi a cikinsa.
  3. Zabin aboki babu makawa dole sai an yi tunani.
  4. Mutum yana karfafar addininsa ta hanyar abokantakar muminai, kuma yana raunana shi ta hanyar abokantaka da fasikai.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 204) (4833). سنن الترمذي (4/ 187) (2378). مسند أحمد (13/ 398) (8028). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 433). تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، للمباركفوري (7/ 51). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص250). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 166). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 341).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "Idan ka haɗu da shi to ka yi masa sallama, idan ya kiraka ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka to ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya godewa Allah to ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya to ka duba shi, idan ya mutu to kabi shi (ka bi jana'izarsa)

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ سِتٌّ» قِيلَ: مَا هُنَّ يَا رَسُولَ اللهِ؟، قَالَ: «إِذَا لَقِيتَهُ فَسَلِّمْ عَلَيْهِ، وَإِذَا دَعَاكَ فَأَجِبْهُ، وَإِذَا اسْتَنْصَحَكَ فَانْصَحْ لَهُ، وَإِذَا عَطَسَ فَحَمِدَ اللهَ فَسَمِّتْهُ، وَإِذَا مَرِضَ فَعُدْهُ وَإِذَا مَاتَ فَاتَّبِعْهُ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "Idan ka haɗu da shi to ka yi masa sallama, idan ya kiraka ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka to ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya godewa Allah to ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya to ka duba shi, idan ya mutu to kabi shi (ka bi jana'izarsa)".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi ɗabi'u shida ne: Na farko: Idan ya haɗu da shi ya yi masa sallama da faɗin: Assalamu alaikum, Wato: Aminci ya tabbata agare ku, shi kuma ya dawo da sallama da faɗinsa: Waalaikumus Salam, Wato: Aminci ya tabbata agare ku. Na biyu: Amsa gayyatarsa idan ya gayyace shi dan walima da makamancinta. Na uku: Yi masa nasiha idan ya nemeta, kada ka yi masa yaudara ko ka yi masa algus. Na huɗu: Idan ya yi atishawa sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah, to ka gaishe shi da faɗin: (Yarhamukallah) Allah Ya yi maka rahama, shi kuma ya amsa yana mai cewa: Allah Ya shiryar da ku kuma ya gyara zuciyarku. Na biyar: Ya gaishe shi kuma ya ziyarceshi idan ya yi rashin lafiya. Na shida: Ya yi masa sallah idan ya rasu, kuma ya bi jana'izarsa har sai an binne shi.

Fa’idoji
  1. Shaukani ya ce: Abin nufi da faɗinsa: (Haƙƙin musulmi) cewa barinsa bai kamata ba, kuma aikatashi yana zama kodai wajibi ko mandubi mai ƙarfi mai kama da wajibin da barinsa ba ya kamata.
  2. Maida sallama farilla ce ta aini idan wanda aka yi wa sallamar shi kaɗai ne, kuma mutum ɗaya ya isarwa jama'a, amma fara sallama to asali a cikinsa shi ne sunnah.
  3. Ziyarar mara lafiya yana daga haƙƙoƙinsa akan 'yan uwansa musulmai; domin cewa ziyara tana shigar da farin ciki da kewa a zuciyarsa, kuma ita farilla ce ta kifaya.
  4. Wajabcin amsa gayyata muddin dai babu wani zunubi a cikinta; idan ta kasance zuwa walimar angwanci ce to jumhur sun tafi akan wajabcin amsata sai dai inda wani uzuri na shari'a, amma idan ta kasance ba walimar angwanci ba ce to jumhur sun tafi a kan cewa sunnah ce.
  5. Gaishe da mai atishawa wajibi ne akan wanda ya ji godiyar (Allah) ga wanda ya yi atishawa ɗin.
  6. Cikar shari'a da kwaɗayinta a cikin ƙarfafa igiyar zamantakewa da imani da alaƙar soyayya tsakanin ɗaiɗaiku.
  7. (Fasammithu) a cikin wasu bugun: (Fashammithu), da Sin mara 'ya'ya da kuma Shin mai 'ya'ya: Addu'a da alheri da kuma albarka, al-Tashmit an ce a cikin ma'anarta: Allah Ya nisantar da kai daga dariyar ƙeta, kuma Ya nisantar da kai abinda maƙiyinka zai yi maka dariyar ƙeta da shi, Tasmit kuma ma'anarsa: Allah Ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 1705) (2162). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 7). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (3/ 128). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 327).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar

عن أبي صِرْمة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ ضَارَّ ضَارَّ اللهُ بِهِ، وَمَنْ شَاقَّ شَقَّ اللهُ عَلَيْهِ».
Daga Abu Sirmah - Allah Ya yarda da shi - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi gargaɗi game ga shigar da cuta ga musulmi, ko riskar da wahala a gareshi a kowane al'amari daga al'amauransa; a ransa ko a dukiyarsa ko a iyalansa, kuma cewa wanda ya aikata hakan Zai yi masa sakayya, Zaiyi masa uƙuba daga jinsin aikinsa.

Fa’idoji
  1. Haramcin cutar da musulmi da riskar da wahala a gareshi.
  2. Kamun Allah ga bayinsa.
Madogara

سنن أبي داود (5/ 477) (3635). سنن الترمذي (3/ 495) (1940). سنن ابن ماجه (3/ 432) (2342). مسند أحمد (25/ 34) (15755). مساوئ الأخلاق، للخرائطي (ص: 274) (583). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، للبسام (7/ 445). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 396). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 261).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com