Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba wata rana sai ya ce: "Shin wane ya zo ne?" suka ce: A'a, ya ce: "Shin wane ya zo ne?" Suka ce: A'a, ya ce: 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi, kuma cewa sahun farko yana kan kwatankwacin sahun mala'iku, da ace kun san falalarsa da kun yi gaggawarsa. Lallai sallar namiji tare da namiji tafi tsarki daga sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tsarki daga sallarsa tare da namiji ɗaya, abinda ya yawaita to shine mafi soyuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -".
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.