La yukallifu Allahu nafsan illa wusAAaha laha ma kasabat waAAalayha ma iktasabat rabbana la tuakhithna in naseena aw akhtana rabbana wala tahmil AAalayna isran kama hamaltahu AAala allatheena min qablina rabbana wala tuhammilna ma la taqata lana bihi waoAAfu AAanna waighfir lana wairhamna anta mawlana faonsurna AAala alqawmi alkafireena
Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi · QuranEnc.com · version 1.2.2. Rubutun boko shi ne wanda Tanzil ke rarrabawa. Sabīl bai duba ko ɗaya daga cikinsu ba.
An nuna shi cikakke, daga Alƙur’ani 2:286. A bugun takarda an gajarta wannan rubutu. Layukan bugun takarda da ke ƙasa an rubuta su ne don gajeren rubutun.