Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 98

At-Tawba 9:98

التوبة

وَمِنَ ٱلْأَعْرَابِ مَن يَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ مَغْرَمًا وَيَتَرَبَّصُ بِكُمُ ٱلدَّوَآئِرَ ۚ عَلَيْهِمْ دَآئِرَةُ ٱلسَّوْءِ ۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Ma’ana

Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda[1] suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce, kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.

[1] Ƙauyãwã kashi biyu ne: Akwai wãwãye munãfukai mãsu ganin addĩni yã ɗõra musu nauyin biyan zakkã da sauran ayyukan alheri, sunã ɗaukar sa kamar tãra da biyan kakkarai. Kuma akwai ƙauyãwa mãsu hankali sun sani Annabi manzo ne daga Allah, sunã ɗaukar abin da addĩni ya azã musu duka ibãda ne, sunã fãtar kusanta da shi zuwa ga Allah, Ubangjinsu. To su mutãnen ƙwarai ne, zã su shigã Aljanna.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net