At-Tawba 9:65
التوبةوَلَئِن سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ ۚ قُلْ أَبِٱللَّهِ وَءَايَـٰتِهِۦ وَرَسُولِهِۦ كُنتُمْ تَسْتَهْزِءُونَ
Kuma lalle ne, idan ka tambaye,[1] su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"
[1] Ana a cikin tafiya zuwa Tabũka sai wasu mutãne daga cikin munãfukai suka ce wa junansu, "Wannan Yana zaton ya ci gidajen Rumawa da Biranensu? faufau." Sai Allah Ya sanar da AnnabinSa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) abin da suka faɗa. Sai ya ce: "Ku zo mani da waɗannan mutãne." Da suka je masa ya ce musu 'Kun ce kaza da kaza.' Sai suka yi rantsuwa da cewa: ba mu kasance ba sai muna hĩra muna wãsã.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net