Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 38

At-Tawba 9:38

التوبة

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَا لَكُمْ إِذَا قِيلَ لَكُمُ ٱنفِرُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱثَّاقَلْتُمْ إِلَى ٱلْأَرْضِ ۚ أَرَضِيتُم بِٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا مِنَ ٱلْـَٔاخِرَةِ ۚ فَمَا مَتَـٰعُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ إِلَّا قَلِيلٌ

Ma’ana

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi[1] zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan.

[1] Nauyi zuwa ga ƙasa, watau ku ƙãsa tãshi tsaye balle mã ku fita zuwa yãƙin da aka neme ku da shi (sabõda shi). fita da yãƙi a nan, anã nufin yãƙin Tabũka a cikin lõkacin bazara, kuma bãbu abinci dõmin Allah Ya jarrabi Musulmi, Ya fitar da mũminai da kuma munãfukai, dõmin a san yadda zã a yi ma'ãmala da su. Haka kuma a kõwane lõkaci Allah Yakan sanya wani abin jarraba na wahala a cikin Musulmi dõmin Ya bambanta mũminai daga munãfukai.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net