Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 34

At-Tawba 9:34

التوبة

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِنَّ كَثِيرًا مِّنَ ٱلْأَحْبَارِ وَٱلرُّهْبَانِ لَيَأْكُلُونَ أَمْوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلْبَـٰطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۗ وَٱلَّذِينَ يَكْنِزُونَ ٱلذَّهَبَ وَٱلْفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Ma’ana

Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr[1] da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.

[1] Jam'in Hibru watan malamin Yahũdãwa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net