Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 31

At-Tawba 9:31

التوبة

ٱتَّخَذُوٓا۟ أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَـٰنَهُمْ أَرْبَابًا مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَٱلْمَسِيحَ ٱبْنَ مَرْيَمَ وَمَآ أُمِرُوٓا۟ إِلَّا لِيَعْبُدُوٓا۟ إِلَـٰهًا وَٰحِدًا ۖ لَّآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Ma’ana

Sun riƙi mãlamansu[1] (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama (haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi.

[1] Hibru shi ne mãlamin Yahũdãwa, Ruhubãni mai ibãda wanda ya yanke jin dãɗin dũniya daga kansa sabõda ibãda, daga cikin Nasãra, mabiyan,gefen biyu sun riƙi shũgabanninsu ubanningiji sunã bauta musu, watau sunã yanka musu dõkoki waɗanda ba na Allah ba, sũ kuma sunã bin su a kan haka. Bautar da suke yi wa Uzairu kõ Masĩhu, Ĩsaɗan Maryama dõmin sun ce sũ ɗiyan Allah ne, watau sun zama juz'inSa ke nan. Tsarki ya tabbata ga Allah daga waɗannan siffõfi duka.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net