Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 16

At-Tawba 9:16

التوبة

أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تُتْرَكُوا۟ وَلَمَّا يَعْلَمِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ جَـٰهَدُوا۟ مِنكُمْ وَلَمْ يَتَّخِذُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَا رَسُولِهِۦ وَلَا ٱلْمُؤْمِنِينَ وَلِيجَةً ۚ وَٱللَّهُ خَبِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ

Ma’ana

Kõ kunã zaton[1] a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai? Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa.

[1] Watau kunã zaton ku shiga Aljanna sabõda cewarku, "Mun yi ĩmãni," kawai? Ã'aha! Sai Allah Yã bayyanar da mai gaskiyar ĩmãni game da jihãdi, kuma gaskiyar ĩmãni itace ce rashin sõyayya da wanin Allah da ManzonSa da mũminai, duka wanda ya so wani abu baicinsu, to, bã mũmini ba ne, bã zai shiga Aljanna ba dõmin wai yã yi ĩmãni kawai. Ma'anar son Allah da son Annabi shi ne rashin sãɓa wa umurninSa. Ma'anar son wanin Allah da wanin Annabi, shi ne ka yi abin da wanin nan yake so, alhãli kuwa a wajen yinsa akwai sãɓa wa Allah da Manzon Sa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net