Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 128

At-Tawba 9:128

التوبة

لَقَدْ جَآءَكُمْ رَسُولٌ مِّنْ أَنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُم بِٱلْمُؤْمِنِينَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ

Ma’ana

Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo[1] daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.

[1] Bayãnin rahamar Allah game da aiko Manzõ daga cikin mutãne, cewa wata falala ce a gare su. Kuma shi Manzon nan ɗan'uwansu ne wanda bã ya son su da wani abu sai alheri, idan sun gãne dã sun bĩ shi, kuma idan ba su gãne bã, to, Allah Yã tsare shi daga sharrinsu, kuma Yã isar masa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net