At-Tawba 9:11
التوبةفَإِن تَابُوا۟ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُا۟ ٱلزَّكَوٰةَ فَإِخْوَٰنُكُمْ فِى ٱلدِّينِ ۗ وَنُفَصِّلُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Sa'an nan idan sun tũba[1] kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.
[1] Rukunõnin Musulunci biyar ne: Kalmar shahãda da salla da azumi da zakka da hajji ga Ɗãkin Allah. Ana yãƙar mutum sabõda barin uku daga cikinsu, watau kalmar shahãda da salla da zakka kawai. Kuma uku sunã lazimtar mawãdaci da matalauci. Su ne kalmar shahãda da salla da azumi kawai. Amma zakka da hajji sai ga mai hãlin yi da wadãta.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net