Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 8 · Aya ta 75

Al-Anfaal 8:75

الأنفال

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنۢ بَعْدُ وَهَاجَرُوا۟ وَجَـٰهَدُوا۟ مَعَكُمْ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ مِنكُمْ ۚ وَأُو۟لُوا۟ ٱلْأَرْحَامِ بَعْضُهُمْ أَوْلَىٰ بِبَعْضٍ فِى كِتَـٰبِ ٱللَّهِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌۢ

Ma’ana

Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne waliyyan[1] sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.

[1] Walicci shi ne kusanta da lizimtar wajabcin taimakon jũna.A farkon Musulunci, Musulmi bã su da walicci a kan wani Musulmi, sai idan yã yi hijira zuwa Madĩna. Bãyan cin Makka da wãtsuwar Musulunci sai waliccin Musulmi ya wajaba a kan kõwane Musulmi a inda duk yake, a cikin dũniya, gwargwadon hãli, amma kuma a cikin haka mafi kusantar zumuntã shi ne mafi cancanta da waliccin kõwane Musulmi, har dai ga abin da ya shãfi hãlãye na zaman mutum kamar aure da gãdo, da sauransu, kamar yadda littattafan sunna suka bayyana, a can cikin bãbin walicci.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Anfaal

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net