Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 8 · Aya ta 72

Al-Anfaal 8:72

الأنفال

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَهَاجَرُوا۟ وَجَـٰهَدُوا۟ بِأَمْوَٰلِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَوا۟ وَّنَصَرُوٓا۟ أُو۟لَـٰٓئِكَ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَآءُ بَعْضٍ ۚ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَلَمْ يُهَاجِرُوا۟ مَا لَكُم مِّن وَلَـٰيَتِهِم مِّن شَىْءٍ حَتَّىٰ يُهَاجِرُوا۟ ۚ وَإِنِ ٱسْتَنصَرُوكُمْ فِى ٱلدِّينِ فَعَلَيْكُمُ ٱلنَّصْرُ إِلَّا عَلَىٰ قَوْمٍۭ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُم مِّيثَـٰقٌ ۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

Ma’ana

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira[1] ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.

[1] A farkon Musulunci hijira sharaɗi ce ga shiga cikin waliccin Musulmi, amma bãyan da Musulunci ya yi ƙarfi, hijira ba ta zama sharaɗi ba, sai dai tanã wajaba ga Musulmi ya tashi daga inda bã ya iya tsare addininsa zuwa ga inda yake iya tsare shi, matuƙar bãbu wata wahala mai tsanani. Ana taimakon Musulmin da bai yi hijira ba ga abin da bai shãfi warware alkawarin Musulmi ba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Anfaal

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net