Al-Anfaal 8:67
الأنفالمَا كَانَ لِنَبِىٍّ أَن يَكُونَ لَهُۥٓ أَسْرَىٰ حَتَّىٰ يُثْخِنَ فِى ٱلْأَرْضِ ۚ تُرِيدُونَ عَرَضَ ٱلدُّنْيَا وَٱللَّهُ يُرِيدُ ٱلْـَٔاخِرَةَ ۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Bã ya kasancewa[1] ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
[1] Bayan da Musulmi suka ci nasara a Badar, suka kama Kuraishãwa a cikinsu har da Abbas baffan Annabi. Sai Annabi ya shãwarci Sahabbansa ga abin da zã su yi da kãmammu. Abubakar ya ce wa Annabi, "Mutãnenka ne, ka sake su." Sa'an nan ya nemi Umar shãwara, ya ce masa: "Ka kashe su." Sai ya karɓi fansa daga gare su. Bãyan haka Alƙur'ãni ya sauka da ƙarfafa ra'ayin Umar na a kashe su, ya fi. Amma tun da an riga an zartar da fansar, shĩ ke nan.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net