Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 8 · Aya ta 41

Al-Anfaal 8:41

الأنفال

وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّمَا غَنِمْتُم مِّن شَىْءٍ فَأَنَّ لِلَّهِ خُمُسَهُۥ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِى ٱلْقُرْبَىٰ وَٱلْيَتَـٰمَىٰ وَٱلْمَسَـٰكِينِ وَٱبْنِ ٱلسَّبِيلِ إِن كُنتُمْ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ وَمَآ أَنزَلْنَا عَلَىٰ عَبْدِنَا يَوْمَ ٱلْفُرْقَانِ يَوْمَ ٱلْتَقَى ٱلْجَمْعَانِ ۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Ma’ana

Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi[1] ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.

[1] Daga farkon sũrar har zuwa a nan, anã bayãnin cewa ganĩmar Badar bã ta kõwa ba ce fãce Allah da ManzonSa; to, a nan Yanã bayãyin yadda zã a raba dũkiyar, kuma wannan rabon, ya zama sunna ga dukkan dũkiyar ganĩma da Musulmi suka sãmu da yãƙi kõ hari.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Anfaal

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net