Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 8 · Aya ta 30

Al-Anfaal 8:30

الأنفال

وَإِذْ يَمْكُرُ بِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِيُثْبِتُوكَ أَوْ يَقْتُلُوكَ أَوْ يُخْرِجُوكَ ۚ وَيَمْكُرُونَ وَيَمْكُرُ ٱللَّهُ ۖ وَٱللَّهُ خَيْرُ ٱلْمَـٰكِرِينَ

Ma’ana

Kuma a lõkacin da waɗanda[1] suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.

[1] Ƙuraishãwa suka tãru sunã shãwarar yadda zã su yi da Muhammadu; kõ su ɗaure shi a cikin gida, kõ su kashe shi, kõ su kõre shi. Ra'ayinsu ya tsaya ga su kashe shi da zãɓaɓɓun mutãne daga kõwace ƙabĩla yadda danginsa, Banĩ Hãshim, bã su iya faɗa da dukkan Lãrabãwa, har su kõma ga diyya. A rãnar da suka shirya kashe shi, Allah Ya umurce shi da hijira zuwa Madĩna. A lõkacin da ya fita daga gidansa ya iske su tsaitsaye, sunã barci, ya zuba turɓãya a kunnuwansu, sa'annan ya shige suka tafi tãre da Abũbakar, suka sauka a cikin kõgon dũtsen Thaur. Bãyan kwãnaki uku, suka fita zuwa Madina.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Anfaal

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net